Connect with us

Kasuwanci

An Bukaci Dillalai Da Su Rage Farashin Kayan Abinci

Published

on

Gwamnatin tarayya ta yi kira ga masu siyar da kayan abinci da su rage farashin kayan domin rage tasirin hauhawar farashin kayayyaki da tsadar kayan abinci ga ‘yan Najeriya.

Ministan noma da samar da abinci Alhaji Abubakar Kari ne ya yi wannan roko a karamar hukumar Ringim ta jihar Jigawa a bikin ranar noman alkama na shekarar 2025 da gwamnatin jihar Jigawa ta shirya.

Ministan wanda ya bayyana yadda wasu marasa kishin kasa ke je fa masu amfani da kayan abinci cikin rudami, ya bukaci masu kishin kasa da su nuna yadda ake ci gaba da samun ragi farashin kayan abinci a bangarori daban daban.

“Gwamnatin tarayya tana sane da yadda farashin kayan abinci ya ragu sosai a manyan kasuwanni, musamman na kayan masarufi kamar su gari, shinkafa, fulawa da spaghetti.

“Duk da haka, abin damuwa ne yadda ’yan kasuwa da yawa, masu yin burodi, da masu shaguna suka ki yin la’akari da wannan ragi na farashin, wanda hakan ya hana ‘yan Nijeriya samun sassaucin da ya kamace su.

“A watannin da suka gabata, masu ruwa da tsaki a harkar samar da abinci sun nuna damuwa kan tashin farashin kayayyakin abinci amma yanzu farashin ya ragu.

“Misali, farashin fulawa ya ragu daga Naira 81,000 a kowane buhu zuwa kasa N60,000 da Spaghetti daga Naira 20,000 zuwa Naira 15,000, don haka adalci ne kuma masu amfani da su sun ci gajiyar wannan ragi.

“Gwamnati ta kuduri aniyar tabbatar da samar da abinci kuma za ta ci gaba da hada hannu da masu ruwa da tsaki domin magance wannan matsala.

“Don haka ina kira ga daukacin ’yan kasuwa da su nuna halin da ake ciki a kasuwanni a halin yanzu a farashinsu, kuma su yi aiki da gaskiya don saukaka wa ‘yan Najeriya.

“Cutar da masu ‘yan Nijeriya a lokacin da ake buƙatar taimako shine mafi rashin kishin ƙasa kuma ba za a yarda da shi ba,” in ji Ministan.

Ya sanar da bayar da gudunmawar injunan ban ruwa dubu goma, dana feshi dubu goma, da lita dubu goma na maganin ciyawa, da sauran lita dubu goma na maganin kwari, da buhunan takin gargajiya, da sauran kayayyaki na Naira biliyan biyar domin tallafawa manoma a jihar Jigawa.

A nasa jawabin gwamna Umar Namadi ya yabawa gwamnatin tarayya bisa tallafin da take baiwa manoman jihar.

Ya ce an fara samun sauyi a harkar noman alkama a jihar Jigawa a shekarar da ta gabata inda gwamnatin tarayya ta kebe kayan noma na musamman ga manoma dubu takwas bisa tallafin kudi.

Ya ce manoman sun noma hekta dubu arba’in na alkama domin karawa kokarin gwamnatin tarayya, ya ce gwamnatin jihar ta tallafa wa manoma 16,454 da rancen Naira biliyan 2.2, wanda suka amince za su biya bayan girbi.

Gwamna Namadi ya ce aikin ya samu nasara, inda aka samu farfadowar kashi 80 cikin 100 kuma ya jawo kudaden shiga sama da Naira biliyan 8 ga tattalin arzikin jihar.

Usman Muhammad Zaria

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai1 week ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara