Labarai
Gwamnatin Tarayya Ta Bai Wa Jihar Jigawa Kayayyakin Noma Na Sama Da Naira Biliyan 5
Gwamnatin tarayya ta ce ta bai wa gwamnatin jihar Jigawa tallafin kayayyakin noma na sama da naira biliyan 5 domin bunkasa noman abinci a fadin jihar.

Ministan noma da samar da abinci Sanata Abubakar Kyari ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi a garin Dabi da ke karamar hukumar Ringim a bikin ranar manoman alkama ta bana.

Ya bayyana cewa, matakin na daga cikin kudirin gwamnatin tarayya na tallafawa jihar wajen bunkasa noma domin kasuwanci.

Sanata Kyari ya yi nuni da cewa, gwamnatin tarayya ta gamsu sosai da yadda gwamnatin jihar Jigawa da manoma suka yi, na rungumar ayyukan noman rani.

Ministan ya yaba da kokarin gwamnatin jihar Jigawa da manoma, bisa goyon bayan shirin gwamnatin tarayya na bunkasa noman alkama, ta hanyar samar da kayan amfanin gona da dabarun zamani.

A nasa jawabin, Gwamna Umar Namadi ya jaddada kudirin gwamnatin jihar na bullo da wasu tsare-tsare da za su samar da guraben ayyukan yi da wadata kasa da abinci.

A cewarsa, tuni ya sayo taraktoci 300, ingantattun irin shuka, da sauran kayayyakin aikin gona domin noman amfanin gona daban-daban a fadin kananan hukumomin jihar 27.

Tun da farko a jawabinsa na maraba kwamishinan noma da albarkatun kasa na jihar Alhaji Muttaqa Namadi ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta bayar da tan 3,500 na ingantaccen irin alkama, da injinan ban ruwa 10,000 domin tallafawa noman alkama a jihar.

Ministan da mukarrabansa da Gwamna Umar Namadi sun ziyarci gonakin alkama da dama a Yakasawa da Dabi a karamar hukumar Ringim.
Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa, kayayyakin da gwamnatin tarayya ta bayar sun hada da injinan ban ruwa 10,000, da lita 10,000 ta maganin kwari, taki na ruwa da injinan feshi.

Wasu daga cikin manyan baki da suka halarci bikin sun hada da, Darakta Janar na Gidan Rediyon Tarayya FRCN, Dr Mohammed Bulama, da sarakuna da malaman addini, da wakilan kungiyar sarrafa fulawa ta kasa, da manoman alkama da wasu manyan jami’an gwamnati.
Usman Muhammad Zaria
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
