Labarai
Shirin ACRESAL A Jihar Jigawa Zai Samar Da Fitilu Akan Titunan Garuruwa 6
Shirin bankin duniya na yaki da kwararowar hamada da sauyin yanayi a yakin arewacin kasar nan, ya zabi wasu garuruwa 6 a jihar Jigawa da za a sanya wa fitulun haska tituna masu amfani da hasken rana.
Shugaban shirin na jihar Jigawa, Alhaji Yahaya Muhamamad Uba Kafin Gana ya bayyana haka ga manema labarai a Dutse, babban birnin Jihar.
Yana mai cewar, a yanzu haka ma tuni an zabi karin wasu garuruwa 60 domin basu bashin kudi marar ruwa.
A don haka, ya bukaci wadanda aka baiwa bashin a baya da su tabbatar sun biya domin wasu su amfana.
Alhaji Muhammad Uba yace Gwamna Umar Namadi ya amincewa shirin ACRESAL sayo karin injinan yashe kogi guda 2, wadanda za a rika amfani da su wajen yashe kogin Hadejia, domin samun saukin sarrafa ruwan kogi don hana ruwa shiga gonaki.
A cewarsa, ACRESAL da ma’aikatar kare muhalli ta jihar za su reni dashen itatuwa miliyan biyar da dubu dari biyar a bana, domin yaki da zaizayar kasa.
Shugaban shjirin na ACRESAL ya kara da cewar a yanzu haka ACRESAL tana gudanar da biyan diyyar naira miliyan 187 ga wadanda aikin zaizayar kasa ya shafi kadarorinsu a unguwannin Dan Masara da kuma Kalgo dake karamar hukumar Dutse.
Usman Mohammed Zaria
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai1 day ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
