Connect with us

Ilimi

Gwamnatin Jihar Kano Ta Fara Rangadin Tantance Yaran Da Ba Sa Zuwa Makaranta

Published

on

Ma’aikatar ilimi ta jihar Kano ta fara rangadin tantancewa a kauyukan jihar, gabanin shirin wayar da kan al’umma game da yaran da ba su zuwa makaranta.

Ziyarar na da nufin gano musabbabin wannan matsala tare da nemo mafita ta hanyar hada kai tsakanin al’umma.

Kididdigar da Asusun yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya fitar na nuna da cewa, Kano tana da kimanin yara 837,479 da ba sa zuwa makaranta, adadi mai ban mamaki da jihar ke kokarin magancewa.

 

Tawagar tantancewar, karkashin jagorancin jami’a mai kula da ilimin yara mata ta jihar, Hajiya Amina Kassim, ta ziyarci kauyuka da dama, inda ta tattauna da iyaye, da shugabannin gargajiya, da malaman addini.

Tawagar ta gano muhimman abubuwan da ke haddasa  yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a yankunan karkara, ciki har da talauci, da rashin tsaro, da kuma al’adun zamantakewa”

Mataimakin shugaban kwamitin gudanarwa na makarantun jihar  SBMC, Alhaji Garba Adamu Wudil, ya ce ta hanyar hada kai da al’ummomin yankin da masu ruwa da tsaki, gwamnati na da burin kara fahimtar matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta da kuma kokarin samar da ingantaccen ilimi ga kowa da kowa.

Hakimin kauyen Kafin Malamai a karamar hukumar Garko Mukhtar Aliyu da wakilin hakimin kauyen Bange na Wudil Ya’u Ibrahim Bange sun yabawa kokarin gwamnati mai ci na gyara fannin ilimi.

Sun yi kira ga gwamnati da ta kara samar da karin makarantun sakandire a cikin al’umma domin daukar adadin daliban da suka kammala karamar sakandare (JSS) duk shekara.

Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa, rangadin tantancewar wani muhimmin mataki ne na samar da ingantattun dabaru don rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a jihar Kano.

Daga Khadija Aliyu

Labarai

Labarai1 day ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai1 day ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai5 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi6 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai1 week ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai1 week ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai1 week ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai1 week ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai1 week ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai1 week ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara