Labarai
Shirin ACRESAL Na Jihar Jigawa Zai Biya Diyar Filaye Da Gidaje Na Miliyoyin Naira
Hukumar kula da farfado da yanayi ACRESAL ta jihar Jigawa ta fara biyan diya ga masu filaye, da gonaki, da gidaje, na sama da naira miliyan 187 ga gidajen Danmasara, da Kargo da Yalwawa da shirin kare zaizayar kasa ya shafa.
Shugaban kwamitin gudanarwa na ACRESAL na jiha kuma babban sakatare na ma’aikatar muhalli Dr Abdullahi Umar Namadi ya bayyana haka a sakateriyar JARDA Dutse.
Dakta Abdullahi Umar Namadi ya bukaci wadanda aka biya diyar da su yi amfani da kudaden yadda ya kamata.
Tun da farko a nasa jawabin, jami’in kula da ayyukan na jiha, Alhaji Yahaya Muhammad Uba Kafingana, ya ce an kokarin ganin an tabbatar da adalci, wajen biyan wadanda abin ya shafa.
Ita ma jami’ar kula da shirin ingantacciyar zamantakewa na Safely Lively Hood, Hajiya Zainab Baba Santali ta ce, za a biya diyar da mutane 481 a Kargo da Danmasara.
Zainab Baba Santali, ta yi nuni da cewa, an bai wa marasa galihu da nakasassu 360 akuya uku uku, da kuma tsabar kudi naira dubu dari kafin a fara aikin da bankin duniya ya amince na bai wa shirin ACRESAL tallafi.
Usman Muhammad Zaria
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
