Connect with us

Labarai

Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Jigawa Ya Raba Sama Da Miliyan 75 Ga Marasa Galihu

Published

on

Gwamnatin Jihar Jigawa ta ce za a ci gaba da bada tallafi ga al’umma a dukkan mazabu 30 na ‘yan majalisar dokokin Jihar.

Gwamnan Jihar Malam Umar Namadi ya bada wannan tabbacin a lokacin da yake kaddamar da bada tallafi ga al’ummar karamar hukumar Miga wanda Shugaban majalisar dokokin Jihar, Alhaji Haruna Aliyu Dangyatin ya raba fiye da Naira Miliyan 75 ga masu karamin karfi.

Malam Umar Namadi, ya  yaba da tsarin bada tallafin ga al’ummar karamar hukumar ta Miga.

A cewarsa, tsarin bada wannan tallafi da kakakin majalisar ya yi ya  dace da kudirorin gwamnatin jihar 12.

Yana mai nuni da cewar, a kowacce Karamar Hukuma  za a kaddamar da irin wannan tallafi domin bunkasa tattalin arzikin al’umma don su zamo masu dogaro da kai.

Namadi, ya ce bullo da tsarin bada tallafin  ya nuna cewar ‘yan majalisar Jihar suna tare da al’ummarsu.

Shi kuwa a nasa jawabin, Kakakin majalisar dokokin jihar Jigawan Alhaji Haruna Aliyu Dangyatin ya ce rabon tallafin ya tasamma fiye da Naira Miliyan 75 wanda al’ummar mazabar Miga ne za su ci moriyar tsarin.

Ya ce tallafin zai basu damar kama sana’oi daban daban domin su zamo masu dogaro da kai.

Dangyatin, ya kuma bayyana cewar mutane kusan 2000 ne za su amfana da tallafin kudaden domin bunkasa tattalin arzikinsu.

Kakakin majalisar, ya kuma godewa Gwamna Umar Namadi bisa kyawawan kudurorinsa,  gami da kulawarsa wajen ciyar da al’ummar jihar gaba.

Usman Mohammed Zaria

Labarai

Labarai1 day ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai1 day ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai5 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi6 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai1 week ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai1 week ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai1 week ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai1 week ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai1 week ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai1 week ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara