Labarai
Shugaba Tinubu Ya Jinjinawa ‘Yan Najeriya Mazauna Kasashen Waje Bisa Nuna Halin Dattaku
Shugaba Bola Tinubu ya bayyana farin cikinsa bisa rahotanin da ya samu game kyawawan dabi’u da ‘yan Nijeriya mazauna kasashen waje suke nunawa a kasashen da suke, yana mai cewa hakan zai zaburar da matasa kan dabi’un da ke kara martabar kasa.
Shugaban ya yabawa ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje yayin da ya karbi wasiku daga jakadan kasar Kanada a Najeriya, Pasquale Salvaggio, da jakadan Saliyo, Dr Julius F. Sandy, a fadar gwamnati.
Har ila yau, shugaba Tinubu ya karbi wasikun amincewa da nuna gamsuwa daga Legesse Geremew Haile, jakadan kasar Habasha a Najeriya, da Archbishop Michael Francis Crotty, shugaban Bishop Bishop na fadar Vatican a Najeriya.
Babban Kwamishinan na Kanada ya shaida wa Shugaba Tinubu cewa ’yan Najeriya suna da himma a fannin ilimi, da wasannin motsa jiki, da kimiyya, da lafiya, da kasuwanci a kasarsa.
Ya ce ‘yan Najeriya a Kanada suna nuna kyawawan dabi’u da wayewa, da kwazo yayin cimma burinsu.
Salvaggio, wanda a baya ya yi aiki a Ghana da Cote’Ivoire, ya ce Kanada na neman fadada sha’awarta a kan man fetur da iskar gas, da al’amuran da suka shafi fasahar zamani, da noma, a dangantakar ta Najeriya.
Shugaba Tinubu ya yaba da nasarorin da ‘yan Najeriya suka samu a kasashen waje, yana mai bayyana su a matsayin abin zaburarwa ga mutane da dama.
A wani taron da ya yi da babban jakadan Saliyo kuwa, shugaba Tinubu ya tabbatar da cewa, muradin Najeriya na ci gaban gabar tekun Yamma da Afirka shi ne abin da ya sa a gaba.
Shugaban ya shaida wa jakadan cewa jarin da Najeriya ta yi a Saliyo na tsawon shekaru da dama ya taimaka wajen ci gaban Afirka da kuma inganta dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.
Jakadan ya godewa shugaban kasar bisa goyon bayan da Najeriya ke bayarwa wajen cigaban kasarsa.
Ya ce “A Saliyo, ‘yan Najeriya sun fi ‘yan kasar yin kasuwanci, yawancin malamai a makarantu ‘yan Najeriya ne, babu bambanci tsakanin dan Najeriya da dan Saliyo idan kana tafiya a kan titin Freetown.”
“Muna bukatar ci gaba da neman zaman lafiya a nahiyarmu, ya kamata mu hada karfi da karfe wajen samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, kalubalen da muke fuskanta a Afirka shi ne rashin tsaro, wanda ke hana ci gaba, ba mu da wanda zai kawo mana zaman lafiya, ssai in mun yi aiki tukuru.” in ji shi.
Daga Bello Wakili
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
