Connect with us

Labarai

Mahukunta Gandun Daji Na Hadejia Sun Kai Ziyarar Aiki Hukumar NOA

Published

on

Hukumar kula da gandun daji na Hadejia ta ce wuraren shakatawa na kasa suna taka rawar gani ta fuskar kiyaye halittu, da magance matsalolin sauyin yanayi, da inganta bincike, da ci gaba, gami da samar da ayyukan yi a Najeriya.

Mukaddashin jami’in kula da gandun dajin, Mista Jonah Moses ya bayyana haka a lokacin da ya kai ziyarar neman shawarwari ofishin wayar da kan jama’a na kasa da ke Dutse, babban birnin jihar Jigawa.

Ya nanata cewa al’umma za su kara fahimtar fa’idojin irin wadannan wurare ne kadai idan Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta Kasa NOA, ta taimaka wajen fadakarwa ko ilmantar da jama’a.

Jonah Moses ya bayyana cewa, sun kawo ziyarar ce domin ganawa da masu ruwa da tsaki irin su hukumar ta NOA, wadanda za su iya taimakawa wajen fahimtar da jama’a game da gandun  daji na Hadejia.

Da yake mayar da martani, Daraktan Hukumar Wayar da Kan Jma’a ta kasa NOA na jihar Jigawa, Malam Ahmad Tijjani Ibrahim ya yabawa mai kula da gandun dajin na Hadejia da tawagarsa bisa da  kwazon da suke nuna wajen tafiyar da ayyukansu.

Ya kara da cewa hukumar ta ba da fifiko kan batun sauyin yanayi, inda ta samar da sashen kula da muhalli, da yanayi, da  makamashi.

Shugaban hukumar ta NOA ya tabbatar wa tawagar cewa a shirye hukumar ta ke na zaburar da al’ummar kasa game da ayyukan gandun dajin.

Usman Muhammad Zaria

Labarai

Labarai14 hours ago

Sauye-sauyen Da Tinubu Ya Samar Ya Haifar Da Cigaba A Jihohi – Namadi

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan matakan da...

Labarai18 hours ago

Jigawa Ta Yi Nazarin Sabbin Tsare-tsaren Masaukin Alhazai A Saudiyya

Daga Usman Muhammad Zaria Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ce tana nazarin hanyoyin inganta jin daɗin alhazai...

Labarai2 days ago

Kano: Kotu Ta Umarci A Lalata Buhunan Fulawa Sama Da 400

Daga Khadijah Aliyu  Wata kotu a Jihar Kano ta bayar da umarnin lalata buhunan fulawa sama da 400 da suka...

Labarai3 days ago

Tinubu Ya Jaddada Ƙudurin Samar Da Ci Gaba A Jigawa

Daga Usman Muhammad Zaria  Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sake jaddada ƙudurin gwamnatinsa na ci gaba da aiwatar da...

Labarai3 days ago

Shugaban Gidan Talabijin Na Katsina Abba Zayyan Ya Yi Murabus

Daga Isma’il Adamu  Babban Manajan gidan talabijin na Jihar Katsina (KTTV), Abba Zayyan, ya miƙa takardar murabus daga muƙaminsa a...

Labarai3 days ago

Namadi Ya Miƙa Buƙatu Uku Ga Tinubu Kan Ci gaban JiharJigawa

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya kai musu...

Labarai3 days ago

Arewa Za Ta Saka Wa Tinubu Da Ruwan Kuri’a A 2027- Yari

Daga Usman Muhammad Zaria  Daraktan Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na APC, Sanata Abdulaziz Yari, ya ce...

Labarai3 days ago

Shettima Ya Bukaci ’Yan Najeriya Su Sake Zaben Tinubu A 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bukaci ’yan Najeriya da su goyi bayan sake zaɓen Shugaba...

Labarai4 days ago

Jigawa Ta Amfana Da Ayyukan Gwamnatin Tinubu – Abdulaziz

Daga Usman Muhammad Zaria Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan harkokin yada labarai da wayar dan...

Labarai4 days ago

Majalisar Kano Za Ta Karɓi Kasafin Kuɗin Shekarar 2027

Daga Khadijah Aliyu  Majalisar Dokokin Jihar Kano na shirin karɓar daftarin kasafin kuɗin shekarar 2027 daga Gwamna Abba Kabir Yusuf...

Mafi Shahara