Connect with us

Ilimi

An Horar da ƙarin Malamai 1000 na Lissafi da Ingilishi A Kabi

Published

on

Gwamnatin jihar Kebbi, ta fara horas da karin malamai dubu daya na sati daya a fannin Lissafi da Ingilishi.

 

Horon da aka yi da nufin baiwa malamai kwakkwaran horo akan ayyuka da isar da saƙon a makarantun jihar musamman a fannin Lissafi da Ingilishi.

 

Da yake jawabi a lokacin da yake bayyana bude horon a Kwalejin Kimiyya da fasaha Umaru Waziri dake Birnin Kebbi, Gwamnan Jihar Kebbi, Kwamared Nasir Idris, ya ce horon ya biyo bayan wani irinsa da aka gudanar a watan Janairun 2024 wanda ya yi tasiri matuka a harkar koyo da koyarwa makarantu.

 

Shugaban ma’aikatan gwamnati na jiha Malami Muhammad Shekare ya wakilta ya jaddada cewa horon zai kasance shiri ne na shekara-shekara domin bunkasa kwazon malamai a jihar.

 

A yayin da yake bayyana ilimi a matsayin ginshikin ci gaba ga kowace al’umma, Gwamna Idris, ya jaddada muhimmancin horas da malamai akai-akai, karfafa gwuiwa, samar da ingantattun kayan koyarwa da kayan aiki, yanayi mai kyau da kuma kafa kwakkwaran tushe ga matasa.

 

Shugaban hukumar kula da ilimin bai daya ta jihar Kebbi (SUBEB), Farfesa Sulaiman Khalid, ya bayyana cewa, gwamnatin jihar ta sanya jari sosai a fannin ilimi a jihar.

 

Ya bayyana cewa, gwamnati ta samar da ajujuwa 789, ajujuwan karatu guda 16,582 da horar da malamai 8,462 da sauransu.

 

Taron horaswar na tsawon mako biyu gwamnatin jihar ta shirya tare da hadin guiwar hukumar bada shawara ta kwalejin kimiyya da fasaha ta Waziri Umaru, Birnin Kebbi.

 

 

COV/Abdullahi Tukur/Wababe

Labarai

Ilimi1 day ago

KANO: Ungogo Ta Ƙaddamar da Shirin Shigar da Yara Makaranta

Daga Khadijah Aliyu Ƙaramar Hukumar Ungogo ta Jihar Kano ta ƙaddamar da wani shirin wayar da kan jama’a domin shigar...

Labarai1 day ago

Jihar Naija Ta Dauki Matakan Gaggawa Sakamakon Bullar Cutar Ebola A Abuja

Daga Aliyu Lawal Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Nijar ta sanya Cibiyar Ayyukan Gaggawa ta Lafiyar Jama’a (PHEOC) cikin shirin ko-ta-kwana,...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya

Daga Bello Wakili  Gwamnatin Tarayya ta fara aiwatar da matakan gaggawa na kare lafiyar jama’a,  bayan tabbatar da bullar cutar...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Fitar Da Naira Biliyan 1.4 Ga Mazabu

Daga Usman Muhammad  Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira biliyan 1.4 wajen aiwatar da ayyukan mazabu...

Fasaha2 days ago

Jigawa Ta Ware Naira Miliyan 380 Don Samar da Wutar Lantarki a Cibiyoyin ICT

Daga Usman Muhammad Zaria  Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira miliyan 380 wajen samarwa...

Labarai2 days ago

’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano

Daga ABDULLAHI JALALUDDEEN, KANO Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama wani mutum da ake zargi da aikata fashi da...

Labarai2 days ago

2027: Ombugadu Ya Yi Alƙawarin kawo Ƙarshen Rashin Tsaro

Daga ALIYU MURAKI, LAFIA Ɗan takara a zaɓen gwamnan Jihar Nasarawa na jam’iyyar PDP, Dr. Emmanuel Ombugadu, ya yi alƙawarin...

Labarai2 days ago

Tajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14

Daga BELLO WAKILI, Abuja Shugaban Majalisar Wakilai ta Najeriya, Dr. Abbas Tajudeen, ya ce zai bayyana cikakken rahoton nasarorin da...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga

Daga AMINU DALHATU Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana matuƙar damuwarta kan ƙaruwar hare-haren ’yan bindiga a wasu sassan jihar a...

Kasuwanci2 days ago

APC Ta Ce Kebbi Na Tare da Tinubu Dari-bisa-Dari

Daga SANI DUTSINMA Babban Daraktan Yaƙin Neman Zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Sanata Abdulazeez Yari, ya ce...

Mafi Shahara