Labarai
Hukumar Alhazai Ta Jihar Jigawa Ta Sanar Da Wa’adin Rufe Rajistar Hajjin Bana
Hukumar jin dadin Alhazai ta jihar Jigawa ta tsaida ranar 30 ga watan Janairu a matsayin ranar karshe ta rajistan maniyatan aikin hajjin bana.
Darakta Janar na Hukumar, Alhaji Ahmed Umar labbo ya bayyana haka a wata sanarwa da hukumar ta rabawa manema labarai a Dutse.
Alhaji Ahmed Umar Labbo ya ce hakan ya biyo bayan gyare gyaren da hukumar aikin hajji ta kasa NAHCON ta yi a jaddawalin tsarin aikin hajjin na bana.
Ya kara da cewar, hukumar aikin hajji ta kasa ta umarci hukumomin Alhazai na jihohi da su tabbatar sun shigar da kudaden aikin hajjin bana na maniyatansu da suka karba kafin ranar daya ga watan Fabrairun 2025.
Labbo yana mai cewar hukumar tuni ta rabar da kaso 40 na kason kujerunta na aikin hajjin bana, tun daga lokacin da aka fara rijistar maniyatan.
Don haka ya yi kira ga masu niyyar sauke faralin a bana da su tabbatar sun biya kudadensu na ajiya kafin wa’adin da aka dauka.
Ya kuma yaba da goyon bayan da Gwamna Umar Namadi yake bai wa hukumar a kowane lokaci.
Usman Mohammed Zaria
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
