Connect with us

Labarai

Jami’an ‘Yan Sanda 272 Sun Sami Karin Girma A Kano

Published

on

 

Kwamishinan ‘Yan sandan Jihar Kano, Salman Dogo Garbaya ja hankalin jami’an rundunar  jihar su 272 da suka sami karin girma da su kasance masu kishin kasa, da kwazo da jajircewa wajen gudanar da ayyukansu.

CP Salman Dogo Garba ne ya bayyana haka ne  a lokacin da yake bai wa  jami’an shaidar karin a hedikwatar ‘yan sanda da ke Bompai, a Kano.

Ya bukace su da su sauke nauyin  da aka dora musu, ta hanyar kula da hakkin al’umma da kuma kare dukiyoyinsu.

“Sabbin mukamanku suna tattare  ne da sabbin ayyuka da ke bukatar kishin kasa, da sadaukarwa wajen yi wa al’umma hidima.” Inji Garba.

“Ina so in tunatar da ku cewa, wannan wani kalubale ne a gare ku. Yayin da kuke samun karin girma, ayyukanku ne  suke karuwa. Ina yi muku fatan samun nasara a yayin ayyukanku.”

Kwamishinan ya ce al’ummar Kano da ma ‘yan Najeriya na sa ran abubuwa da dama daga gare su, inda ya bukaci jami’an da aka kara musu girma da su jajirce wajen gudanar da ayyukansu bisa tsoron Allah.

Ya ce jami’an da aka kara wa girma sun hada da manyan Sufetan ‘yan sanda 4 da suka sami mataimakin kwamishinan ‘yan sanda AC, sai  Sufetan ‘yan sanda 50 da suka sami mukamin babban Sufetan ‘yan sanda, da mataimakan Sufurtandan ‘yan sanda 32 da suka  zama Supretendad, da kuma jami’ai 182 da suka zama  mataimakan Sufurtandan ‘yan sanda.

Iyalan  jami’an da suka sami karin girman na daga cikin manyan bakin da suka halarci taron.

 

Abdullahi Jalaluddeen

Labarai

Labarai23 hours ago

Kano: Kotu Ta Umarci A Lalata Buhunan Fulawa Sama Da 400

Daga Khadijah Aliyu  Wata kotu a Jihar Kano ta bayar da umarnin lalata buhunan fulawa sama da 400 da suka...

Labarai2 days ago

Tinubu Ya Jaddada Ƙudurin Samar Da Ci Gaba A Jigawa

Daga Usman Muhammad Zaria  Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sake jaddada ƙudurin gwamnatinsa na ci gaba da aiwatar da...

Labarai2 days ago

Shugaban Gidan Talabijin Na Katsina Abba Zayyan Ya Yi Murabus

Daga Isma’il Adamu  Babban Manajan gidan talabijin na Jihar Katsina (KTTV), Abba Zayyan, ya miƙa takardar murabus daga muƙaminsa a...

Labarai2 days ago

Namadi Ya Miƙa Buƙatu Uku Ga Tinubu Kan Ci gaban JiharJigawa

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya kai musu...

Labarai2 days ago

Arewa Za Ta Saka Wa Tinubu Da Ruwan Kuri’a A 2027- Yari

Daga Usman Muhammad Zaria  Daraktan Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na APC, Sanata Abdulaziz Yari, ya ce...

Labarai2 days ago

Shettima Ya Bukaci ’Yan Najeriya Su Sake Zaben Tinubu A 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bukaci ’yan Najeriya da su goyi bayan sake zaɓen Shugaba...

Labarai3 days ago

Jigawa Ta Amfana Da Ayyukan Gwamnatin Tinubu – Abdulaziz

Daga Usman Muhammad Zaria Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan harkokin yada labarai da wayar dan...

Labarai3 days ago

Majalisar Kano Za Ta Karɓi Kasafin Kuɗin Shekarar 2027

Daga Khadijah Aliyu  Majalisar Dokokin Jihar Kano na shirin karɓar daftarin kasafin kuɗin shekarar 2027 daga Gwamna Abba Kabir Yusuf...

Labarai4 days ago

Yankin Funtua Sun Yi Fitowar Farin Dango A Yakin Neman Zaɓe Na APC- Hamza Faskari

Daga Isma’il Adamu  An bayyana yakin neman zaben jam’iyyar APC a yankin Sanatan Funtua na Jihar Katsina a matsayin nasara,...

Labarai4 days ago

Namadi Ya Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen APC Na 2027

Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya ce an haɗa kwamitocin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa...

Mafi Shahara