Connect with us

Labarai

Kasar Congo Ta Yankewa Sojoji 13 Hukuncin Kisa Bisa Saɓa Dokar Aiki

Published

on

 

Wata Kotu ­a Jamhuriyyar Congo ta zartas da hukuncin kisa kan wasu Sojoji 13 bayan samunsu da laifuka masu alaƙa da kisan kai da sace sacen dukiyoyin jama’a da kuma ragwantaka a fagen daga, yayin mamayar da mayaƙan M23 suka yi wa yankin da suke bai wa kariya.

Yayin zaman kotun na jiya Laraba ne ta zartas da hukuncin kisan kan Sojojin 13, bayan abin kunyar da suka aikata a yankin Lubero na gabashin lardin Kivu, wanda ta ce ya saɓawa horarwar Soji a ƙasar mai fama da rikici na tsawon shekaru, ciki har da hare-haren M23 da ke cika shekaru 3 da farowa.

Akalla sojoji 24 ne suka gurfana gaban kotu yayin hukuncin na jiya, Baya ga wadanda aka yanke wa hukuncin kisa, hudu sun samu hukuncin zaman shekaru 2 zuwa 10 a gidan yari, an kuma wanke wasu shida, sannan an ɗage karar daya don ci gaba da bincike.

Mai gabatar da ƙara a kotun Kabala Kabundi, ya bayyanawa kamfanin dillacin labaru na Reuters cewa an gudanar da shari’ar ce domin tabbatar da ɗorewar ɗa’a da aminci  a tsakanin al’umar kasar da kuma dakarun sojin kasar.

A yayin shari’ar dai dukkanin  wadanda aka gurfanar sun amsa laifinsu, inda da kotun ta baiwa mutum biyar daga cikinsu kwanaki biyar na su ɗaukaka ƙara in sun buƙaci hakan.

 

RFI

Labarai

Labarai12 hours ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ware Sama Da Naira Biliyan 1 Don Bunƙasa Kiwo Da Sana’o’i

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kashe naira biliyan 1.124 domin ginawa da gyara cibiyoyin kiwo...

Labarai13 hours ago

Tinubu Ya Gargadi ’Yan Siyasa Kan Tashin Hankali Gabanin Zaɓen 2027

Daga Bello Wakili  Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gargaɗi ’yan siyasa da magoya bayansu kan guje wa tashin hankali,...

Labarai13 hours ago

Jigawa Ta Amince Da Naira Miliyan 570 Don Inganta Abinci Mai Gina Jiki

Daga Usman Muhammad Zaria  Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da ware naira miliyan 570 a matsayin tallafin haɗin...

Labarai13 hours ago

Jigawa Ta Ware Sama Da Naira Biliyan 1 Ga Ayyukan Samar Da Ruwa

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kashe naira biliyan 1.116 domin gudanar da ayyukan samar da...

Labarai2 days ago

Sauye-sauyen Da Tinubu Ya Samar Ya Haifar Da Cigaba A Jihohi – Namadi

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan matakan da...

Labarai2 days ago

Jigawa Ta Yi Nazarin Sabbin Tsare-tsaren Masaukin Alhazai A Saudiyya

Daga Usman Muhammad Zaria Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ce tana nazarin hanyoyin inganta jin daɗin alhazai...

Labarai3 days ago

Kano: Kotu Ta Umarci A Lalata Buhunan Fulawa Sama Da 400

Daga Khadijah Aliyu  Wata kotu a Jihar Kano ta bayar da umarnin lalata buhunan fulawa sama da 400 da suka...

Labarai4 days ago

Tinubu Ya Jaddada Ƙudurin Samar Da Ci Gaba A Jigawa

Daga Usman Muhammad Zaria  Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sake jaddada ƙudurin gwamnatinsa na ci gaba da aiwatar da...

Labarai4 days ago

Shugaban Gidan Talabijin Na Katsina Abba Zayyan Ya Yi Murabus

Daga Isma’il Adamu  Babban Manajan gidan talabijin na Jihar Katsina (KTTV), Abba Zayyan, ya miƙa takardar murabus daga muƙaminsa a...

Labarai4 days ago

Namadi Ya Miƙa Buƙatu Uku Ga Tinubu Kan Ci gaban JiharJigawa

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya kai musu...

Mafi Shahara