Labarai
An Kama Wata Budurwa Da Ke Jagorantar Masu Satar Waya A Kano
Rundunar ‘yan sanda a jihar Kano ta tarwatsa wata kungiya kalkashin jagorancin wata yarinya mai suna Shamsiyya Adamu, da ke da hannu wajen satar wayar hannu, lamarin da ya kai ga kama biyar daga cikinsu.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana haka a lokacin da yake gabatar da wadanda ake zargin a hedikwatar ‘yan sandan Bompai kano.
Ya tabbatar da cewa an kama Shamsiyya mai shekaru 19 ne a ranar 21 ga watan Disamban 2024, biyo bayan rahotannin satar wayoyin hannu a yankin Unguwa Uku, inda aka rika samun korafe-korafe da dama daga mazauna birnin Kano kan wata budurwa da ake zargin tana satar wayoyin hannu a gidaje.
Ya kara da cewa, bincike ya nuna cewa Shamsiyya, tare da taimakon ’yan damfara da masu aikata laifuka ta yanar gizo, suna kai hari kan matan aure.
“Binciken da aka yi kan sace-sacen wayoyin salula, ya yi sanadiyyar kama Shamsiyya, inda aka gano cewa baya ga satar wayoyi, kungiyar tana da hannu wajen yin amfani da bayanan banki da ake sata wajen fitar da kudi daga asusun wadanda abin ya shafa,” in ji SP Kiyawa.
Kiyawa ya kara da cewa, abubuwan da kungiyar ke yi sun hada da yaudarar matan aure domin sace musu wayoyinsu, inda wani mai keken napep ke jigilar Shamsiyya zuwa wurare daban-daban, yayin da masu laifin ta yanar gizo sun yi amfani da bayanan bankin da aka sata don tara kudade daga asusun ajiyar banki na jama’a.
Wadanda ake zargin sun hada da Shamsiyya Adamu, mai shekaru 19, wacce ita ce shugaba, da Idris Yusuf, dan shekara 23, da Al’asan Dahiru, dan shekara 24, da Abdulmajid Haruna, dan shekara 27, wanda ya sayi wayoyin da aka sace da Salim Auwalu, dan shekara 21 da ya yi amfani da fasahar yanar gizo wajen satar kudi.
An kwato wayoyin hannu guda shida da aka sace daga hannun Abdulmajid.
Kiyawa ya kara da cewa kawo yanzu, masu korafi 30 da suka hada da mata 29 da namiji daya ne suka kai rahoton sace musu wayoyinsu.
Shamsiyya ta amsa laifin satar wayoyi a lokuta daban-daban a cikin shekarar da ta gabata.
Abdullahi Jalaluddeen
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai4 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
