Ilimi
Uwargidan Gwamnan Jihar Kwara Ta Bukaci Dalibai Su Kauracewa Shaye-shaye
Uwargidan gwamnan jihar Kwara, Ambasada Olufolake AbdulRazaq, ta shawarci dalibai da su guji shaye-shayen miyagun kwayoyi, tare da gujewa dukkan wani nau’in tu’ammali da kwaya.
Uwargidan gwamnan ta bayar da wannan shawarar ce a makarantar sakandiren Sarauniya Elizabeth da ke Ilorin a yayin wani taron da kwamitin yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi na jihar Kwara da hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) da ofishin uwargidan gwamnan jihar suka shirya, domin wayar da kan dalibai a jihar, a bikin ranar yaki da tu’ammali da miyagun kwayoyi ta duniya da Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana.
Uwargidan gwamnan wadda kwamishinar lafiya ta jihar Dr Amina Ahmed El-Imam ta wakilta,
ta jaddada mahimmancin dalibai su zama jakadu nagari ta hanyar gujewa miyagun kwayoyi da sauran abubuwan da ba su dace ba.

Ta kuma yi kira ga daliban Makarantu da su wayar da kan sauran daliban game da illolin shaye-shayen miyagun kwayoyi da gujewa cin zarafi ko yaudarar su da shan miyagun kwayoyi.
Uwargidan gwamnan, ta bayyana irin jajircewar da gwamnatin jihar ta yi na ganin ta kawar da tu’ammali da miyagun kwayoyi a tsakanin dalibai.
Ta kuma bukaci daliban da su bai wa ilimi fifiko, inda ta kara da cewa ilimi shi ne abu mafi daraja da za su samu.
Ambasada Olufolake AbdulRazq ta kara karfafawa daliban kwarin guiwa da su mai da hankali kan karatunsu tare da kaurace wa duk wani abu da zai illata rayuwarsu.
Ali Muhammad Rabi’u
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai4 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
