Ilimi
Gwamnatin Jihar Kano Za Ta Kashe Naira Biliyan 3 Wajen Gina Azuzuwa A Makarantu
Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana shirin ta na kashe sama da Naira biliyan 3 wajen gina sabbin azuzuwa a fadin kananan hukumomin jihar 44.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana haka a yayin taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a gidan gwamnati dake Kano.
Ya ce gwamnati na da burin samar da yanayi mai kyau na koyo da koyarwa ta hanyar gina karin ajujuwa da gyara wadanda suka lalace.
Gwamnan ya bayyana cewa za a dauki sama da jami’an tsaro 17,000 aiki a fadin jihar domin tabbatar da tsaron kayayyakin makarantun firamare, inda za a tura mutum 400 a kowace karamar hukuma.
“Za a dauki masu gadi a yankunan da suke domin aiki a makarantun firamare da nufin tabbatar da ganin an kare makarantun yadda yakamata“.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ci gaba da cewa kowace karamar hukuma za ta samu Naira miliyan 25 domin gyara azuzuwa, inda hukumar kula da ilimin bai daya ta kasa za ta sa ido kan aikin domin tabbatar da ingancisa.
Ya kara da cewa zuba jarin ya nuna kudirin gwamnati na inganta ababen more rayuwa da samar da ingantaccen ilimi ga dalibai.
Abdullahi Jalaluddeen
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai4 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
