Labarai
Mun Shirya Tsaf Don Fara Jigilar Alhazan Jihar Jigawa- Ahmad Labbo
Hukumar Jin dadin alhazai ta Jihar Jigawa ta bukaci maniyyatan Jihar su zama cikin shiri domin ana dab da fara jigilar su zuwa kasa mai tsarki don aikin hajjin bana.
Hukumar ta kuma bayyana cewar tuni ta tura Jami’anta da za su tarbi alhazan a kasar Saudi Arabia.
Darakta Janar na Hukumar Alhaji Ahmed Umar Labbo ya bayyana haka a zantawarsa tare da Wakilinmu Usman Mohammed Zaria dake Dutse Babban birnin Jihar.
Ya bayyana cewar shirye-shirye sun kammala domin sun ziyarci filin sauka da tashin jirage na Nuhu Muhammadu Sunusi dake Dutse domin tabbatar da al’amura sun daidaita kamar yadda aka tsara.
Alhaji Ahmed Umar Labbo ya kara da cewar, a zancen da ake yi yanzu an fara tsaftace tare da feshin maganin sauro a sansanin alhazai dake fanisau domin samun walwalar alhazai wajen tantance su.
Game da batun tsaro kuwa, yana mai cewar tuni hukumar ta zauna tare da tattauna da jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki domin samar da tsaro ga alhazai tun daga kananan hukumomin su da sansanin alhazai da kuma filin jirgin da ke Dutse.
Daraktan ya ce tuni wasu daga cikin jami’an hukumar na Jidda, wasu kuma a Madina, yayin da wasu ke garin Makka don tabbatar da ganin Alhazan sun sami kyakkyawar kulawar da ta dace da zarar sun isa kasa mai tsarki.
Labbo, yayi nuni da cewar a kowanne Jirgi akwai rukunin jami’an lafiya da ‘yan jaridu da Malamai masu fadakarwa da za su kasance tare da Alhazai akan kowace gaba ta aikin hajji.
A don haka, ya bukaci maniyyatan jihar da su kasance jakadu na gari tare da kiyaye dokokin kasar nan da na Saudi Arabia, wajen gujewa ddaukr abubuwan da aka haramta ttafya da su.
Darekta Janar din ya kuma yabawa Gwamna Umar Namadi bisa hadin kai da goyon bayan da yake baiwa hukumar don kwalliya ta ci gaba da biyan kudin sabulu.
Usman Mohammed Zaria
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai7 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai7 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai7 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai7 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai7 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
