Connect with us

Labarai

Bellingham Ya Zama Gwarzon Wasan La Liga Na Bana

Published

on

An zaɓi ɗan ƙwwallon Real Madrid, Jude Bellingham a matsayin gwarzon ɗan wasan La Liga na bana a kakar farko da ya yi a Sifaniya.

Bellingham, mai shekara 20, ya ci ƙwallo 19 a babbar gasar tamaula ta Sifaniya, wanda ya taimaka Real Madrid ta lashe kofin bana kuma na 36 jimilla.

Ƙungiyar Santiago Bernabeu ta kare a matakin farko a teburin gasar da tazarar maki 10 tsakaninta da Barcelona ta biyu mai rike da La Liga na bana.

Haka kuma ɗan wasan tawagar Ingila, ya zura ƙwallo hudu a raga a Champions League, inda ƙungiyar da Carlo Ancelotti ke jan ragama ta kai wasan karshe a bana.

RanarAsabar 1 ga watan Yuni Real Madrid za ta fafata da Borussia Dortmund a wasan karshe a gasar ta zakarun Turai.

Tsohon ɗan ƙwallon Dortmund ya yi takarar gwarzon dan wasan La Liga a bana tare da takwaransa, Vinicius Jr da Antoine Griezmann na Atletico Madrid da Artem Dovbyk na Girona da kuma Robert Lewandowski na Barcelona.

Ƙyaftin din ƙungiyoyin dake buga La Liga ne ke yin zaben tare da magoya baya da mahukuntan dake gudanar da ƙyautar.

Bellingham ne ya lashe ƙyautar gwarzon ɗan wasan Bundesliga a 2022/23 a lokacin da yake taka leda a Dortmund, daga baya Real Madrid ta dauke shi kan  kudi Fan miliyan tamanin da takwas da dubu dari biyar kafin fara kakar da aka kammala.

Labarai

Labarai1 hour ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi1 week ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Mafi Shahara