Connect with us

Labarai

An Bayar Da Horo Na Musamman Ga Mahauta A Jihar Kwara

Published

on

An horar da mahauta sama da 300 a fadin kananan hukumomi 16 na jihar Kwara kan yadda ake sarrafa nama da tsaftar muhalli don kare yaduwar cututtuka.

Da yake jawabi a wajen taron horaswar da hukumar da ke kula da kiwon dabbobi ta jihar Kwara tare da hadin gwiwar ma’aikatar noma da raya karkara  da kuma kungiyar Bolaniks suka shirya, Gwamna AbdulRahman AbdulRazq ya ce horon wani bangare ne na kokarin gwamnatin jihar na tabbatar da lafiyar abinci da kuma kare yaduwar cututtukan dabbobi.

Gwamnan wanda  kwamishinan aikin gona da raya karkara ta jihar Misis Oloruntoyosi Thomas ta wakilta,  ya ce shirin zai kuma bayar da  kayayyakin kariya wato PPE kimanin dubu uku ga masu gudanar da kasuwancin kiwo  da mahauta a jihar.

AbdulRazaq ya bayyana cewa horon zai baiwa masu kiwon dabbobi damar samun kwarewa kan inganta lafiyar dabbar Dabbobinsu.

Ya yi nuni da cewa, gwamnatin jihar ta samar da shirin da  zai kwadaitar da jama’a su fara noma a muhallansu domin rage tsadar kayan abinci.

A  jawabinsa Daraktan Kiwon Lafiyar Jama’a na Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kwara, Dokta Oluwatosin Fakayode ya ce shirin an yi shi ne don tabbatar da lafiya ga mutane da dabbobi.

A nata jawabin, daraktan kula da lafiyar al’umma da cututtuka ta sashen dabbobi a ma’aikatar noma da raya karkara ta jihar Kwara, Dr.Idiat Omolola-Amin ta ce shirin an yi shi ne domin tabbatar da tsaftar muhalli a mahauta daban-daban da ke fadin jihar.

Ta ce ma’aikatar za ta ci gaba da wayar da kan jama’a kan bukatar sayen nama a kasuwannin da gwamnati ta amince da su.

 

Ali Muhammad Rabi’u

Labarai

Labarai1 day ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai1 day ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai5 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi6 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai1 week ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai1 week ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai1 week ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai1 week ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai1 week ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai1 week ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara