Labarai
Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Rufe Bankin UBA Kan Kin Biyan Haraji
Hukumar Tara Kudaden Haraji ta Jihar Kaduna (KADIRS) ta raufe rassan bankin UBA kan kin biyan harajin Naira miliyan 14.
KADIRS ta rufe rassan bankin guda shida da ke Kaduna ne bayan hukumar gudanarwar bankin ya gaza biyan harajin da ake bin su, duk da takardun tunatarwar da hukumar aike musu a lokuta daban-daban.
Sakataren Majilisar Gudanarwar kuma Mai ba da Shawara kan Shari’a ta KADIRS, Barista Aysha Muhammad da rakiyar jami’an tsaro ta jagoranci rufe rassan bankin.
A cewarta, hukumar ta dauki matakin ne da nufin karbo bashin kudaden haraji Naira N14,367,322.20k da suke bin bankin daga shekarar 2019 zuwa 2021, kamar yadda dokar hukumar ta tanadar.
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai1 day ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
