Ilimi
Ƴan Sanda Za Su Yi Bincike Kan Makarantar Leads British
Rundunar ƴan sanda a babban birnin tarayya Abuja ta ce ta aika tawagar jami’anta zuwa makarantar Leads British bayan bidiyon yadda wata ɗaliba ke cin zalin ƴar ajinsu ya bazu a shafukan sada zumunta.
Kakakin rundunar, SP Josephine Adeh ta ce rundunar ta san da abin da ya faru kuma tana ɗaukan mataki a kai.
A cewar kakakin, ƴan sandan da aka tura za su gudanar da bincike tare da hana karya doka da oda.
A ranar Litinin ne bidiyon da ke nuna yadda ake cin zalin wata ɗaliba ya karaɗe shafukan sada zumunta lamarin da ya fusata al’ummar kasan nan.
Tuni dai hukumar makarantar ta fitar da sanarwa inda ta nemi yafiyar al’umma da kuma iyayen ɗaliban makarantar sannan ta ce ta soma bincike kan lamarin.
-
Ilimi7 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai2 days ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai6 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai2 days ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
