Labarai
Jirgin Sama Ya Zame Daga Kan Titinsa A Legas
Fasinjojin sun tsallake rijiya da baya, bayan jirgin saman da suka hau ya shige cikin jeji da su a Jihar Legas.
A yayin da ake ruwan sama ne wani jirgin fasinja mallakin kamfanin Dana Air ya zame daga kan titinsa a filin jirgi na Murtala Muhammad da ke Legas, sannan ya ci kasa a cikin jeji.
Hakan ya sa fasinjojin ficewa cikin gaggawa don tsira da rayuwarsu da kuma guje wa abin da ka iya biyowa baya.
Bidiyon abin da ya faru da fasinjojin suka ɗauka bayan sun tsallake rijiya da baya ya nuna tayar gaban jirgin ta nutse a kasa a cikin ciyayi.
Zuwa lokacin hada wannan rahoti dai hukumomi ko kamfanin Dana Air ba su ce komai kan lamarin ba.
Haka zalika babu bayanin cewa wani ya samu rauni ko kuma asarar rai ba.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
