Connect with us

Labarai

INEC Ta Ƙaddamar Da Kwamitin Wayar Da Kai Ga Masu Zaɓe A Kaduna

Published

on

Daga Abdullahi Shettima

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), reshen jihar Kaduna, ta kaddamar da Kwamitin Haɗin Gwiwar Hukumomi kan Ilimantar da Masu Zaɓe da Wayar da Kan Al’umma (SICVEP), domin ƙarfafa ilimantar da masu zaɓe, wayar da kan jama’a da haɗin gwiwar masu ruwa da tsaki gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

Mukaddashin Kwamishinan Zaɓe na jihar, Malam Abba Yahaya, ne ya bayyana hakan yayin taron farko na kwamitin da aka gudanar a Kaduna.

Ya ce kwamitin zai samar da ingantaccen tsarin haɗin gwiwa tsakanin hukumomin gwamnati, ƙungiyoyin farar hula, kafafen yaɗa labarai da sauran masu ruwa da tsaki, domin inganta ilimantar da masu zaɓe da ƙarfafa shigar jama’a cikin harkokin dimokuraɗiyya.

Malam Abba Yahaya ya ce kwamitin zai samar da tsare-tsare na matsakaici da dogon zango kan ilimantar da ‘yan ƙasa da masu zaɓe, tare da gano ƙungiyoyin da za su taimaka wajen gudanar da ayyukan da kuma bai wa hukumar shawarwari kan hanyoyin wayar da kan jama’a.

Ya ƙara da cewa kwamitin zai kuma mayar da hankali wajen rage ƙaurace wa zaɓe, inganta kyawawan halaye tsakanin al’umma da kuma dakile rikice-rikicen zaɓe da sauran maguɗan zaɓe.

Mukaddashin Kwamishinan Zaɓen ya sanar da cewa hukumar ta tsara gudanar da gwajin na’urar tantance masu zaɓe ta BVAS da ɗora sakamakon zaɓe a ranar 28 ga watan Nuwamba, 2026, domin tantance yadda na’urar za ta yi aiki a yanayi daban-daban.

Ya bayyana cewa an zaɓi rumfunan zaɓe biyu a kowace mazabar rajista, inda aka samu jimillar rumfunan zaɓe 510 a faɗin ƙananan hukumomi 23 na jihar Kaduna.

Dangane da aikin rajistar masu zaɓe, ya ce hukumar ta fara raba katunan zaɓe na dindindin (PVCs) ga waɗanda suka yi rajista a kashi na farko da na biyu tun ranar 9 ga Oktoba, 2026, yayin da ake jiran katunan waɗanda suka yi rajista a kashi na uku.

Ita ma shugabar sashen Ilimantar da Masu Zaɓe da Wayar da Kan Jama’a ta INEC a Kaduna, Hajiya Rukayya Sani Imam, ta ƙara haske kan manufofi da nauyin da ke bisa kwamitin haɗin gwiwar.

Ta jaddada muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki wajen kai saƙonnin ilimantar da masu zaɓe da wayar da kan jama’a zuwa sassa daban-daban na jihar.

Hajiya Rukayya ta kuma bayyana buƙatar ci gaba da wayar da kan jama’a domin ƙarfafa masu cancantar kaɗa ƙuri’a su shiga zaɓe, su guji tashin hankali tare da kiyaye ƙa’idojin dimokuraɗiyya.

A nasa ɓangaren, Mukaddashin Kwamishinan Zaɓen ya buƙaci mambobin kwamitin da su gudanar da wannan aiki cikin kishin ƙasa da jajircewa, domin tabbatar da sahihin zaɓe mai gaskiya, haɗa kowa da kowa da zaman lafiya a jihar Kaduna.

Yusuf Zubairu

Labarai

Labarai1 day ago

INEC Ta Ƙaddamar Da Kwamitin Wayar Da Kai Ga Masu Zaɓe A Kaduna

Daga Abdullahi Shettima Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), reshen jihar Kaduna, ta kaddamar da Kwamitin Haɗin Gwiwar...

Labarai2 days ago

An Bukaci Masu Kula da Lafiyar Al’umma Su Rike Ka’idojin Aiki

An bukaci masu aikin kula da lafiyar al’umma da su kasance masu bin ka’idojin sana’arsu tare da kiyaye martabar aikin,...

Labarai3 days ago

NIAS Ta Karrama Namadi Bisa Bunƙasa Harkar Kiwo

Daga Usman Muhammad Zaria  Cibiyar Nazarin Kimiyyar Dabbobi ta Ƙasa (NIAS) ta karrama Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, da...

Labarai4 days ago

Gobara Ta Lalata Shaguna 10 A Jihar Kwara

Daga Ali Muhammad Rabi’u  Wata gobara da ta tashi da tsakar dare ta ƙona shaguna takwas da shagunan kwantena guda...

Labarai4 days ago

Shugaban Majalisar Kano Ya Ƙaddamar Da Sabon Ofishin ’Yan Sanda A Rogo

Daga Khadijah Aliyu Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano, Jibril Ismail Falgore, ya ƙaddamar da sabon ofishin ’yan sanda na shiyya...

Labarai5 days ago

Jigawa: Grand Khadi Ya Fara Rangadin Kotunan Shari’a

Daga Usman Muhammad Zaria  Mukaddashin Babban Alƙalin Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Shari’a ta Jihar Jigawa, Umar Nasir Ahmad, ya fara...

Labarai5 days ago

Za a Gabatarda Zaben Kananan Hukumomi a 2027 a Kaduna

Hukumar Zaɓe ta Jihar Kaduna (KADSIECOM) ta sanar da cewa za a gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a faɗin jihar a...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Kebbi Ta Kammala Shirye-shiryen Tarbar Tinubu

Daga Sani Dutsinma  Gwamnatin Jihar Kebbi ta ce ta kammala shirye-shiryen tarbar Shugaba Bola Ahmed Tinubu, domin halartar gangamin yaƙin...

Labarai1 week ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ware Sama Da Naira Biliyan 1 Don Bunƙasa Kiwo Da Sana’o’i

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kashe naira biliyan 1.124 domin ginawa da gyara cibiyoyin kiwo...

Labarai1 week ago

Tinubu Ya Gargadi ’Yan Siyasa Kan Tashin Hankali Gabanin Zaɓen 2027

Daga Bello Wakili  Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gargaɗi ’yan siyasa da magoya bayansu kan guje wa tashin hankali,...

Mafi Shahara