Connect with us

Labarai

Jigawa Ta Amince Da Naira Miliyan 570 Don Inganta Abinci Mai Gina Jiki

Published

on

Daga Usman Muhammad Zaria 

Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da ware naira miliyan 570 a matsayin tallafin haɗin gwiwa domin sayen muhimman kayan magani da abinci mai gina jiki ta hannun UNICEF, don yaƙi da matsanancin ƙarancin abinci mai gina jiki a tsakanin yara.

Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed ne ya bayyana hakan bayan taron majalisar zartarwar da aka gudanar a gidan gwamnati da ke Dutse.

Ya ce an ware naira miliyan 300 domin sayen abinci na musamman da ake amfani da shi wajen magance  tamowa (RUTF), da kuma madarar magani ta musamman nau’in F75 da F100 domin kula da yaran da ke fama da matsananciyar tamowa.

Ya ƙara da cewa, an ware naira miliyan 270 domin sayen sinadaran ƙarin gina jiki (Multiple Micronutrient Supplements), don magance ƙarancin muhimman sinadarai a jiki da inganta lafiyar al’umma masu rauni.

Kwamishinan ya bayyana cewa, wannan mataki ya biyo bayan samun nasarar kula da yara 15,957 daga cikin 18,122 da aka karɓa a cibiyoyin kula da masu fama da matsananciyar tamowa ba tare da kwantar da su a asibiti ba a faɗin jihar a shekarar 2025, wanda ya kai kashi 88.1 cikin 100.

Ya danganta nasarar da zuba jari mai ɗorewa a shirye-shiryen inganta abinci mai gina jiki, ingantattun hanyoyin jinya da haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin jihar, UNICEF da sauran ƙungiyoyin ci gaba.

Sagir Musa Ahmed ya ce kuɗaɗen za su tabbatar da ci gaba da samun muhimman kayan abinci na musamman, da kuma faɗaɗa damar samun maganin ceton rayuka ga yara masu rauni a ƙananan hukumomi 27 na jihar.

Fassara: Safiyah Abdulkadir 

Labarai

Labarai13 hours ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ware Sama Da Naira Biliyan 1 Don Bunƙasa Kiwo Da Sana’o’i

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kashe naira biliyan 1.124 domin ginawa da gyara cibiyoyin kiwo...

Labarai13 hours ago

Tinubu Ya Gargadi ’Yan Siyasa Kan Tashin Hankali Gabanin Zaɓen 2027

Daga Bello Wakili  Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gargaɗi ’yan siyasa da magoya bayansu kan guje wa tashin hankali,...

Labarai13 hours ago

Jigawa Ta Amince Da Naira Miliyan 570 Don Inganta Abinci Mai Gina Jiki

Daga Usman Muhammad Zaria  Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da ware naira miliyan 570 a matsayin tallafin haɗin...

Labarai14 hours ago

Jigawa Ta Ware Sama Da Naira Biliyan 1 Ga Ayyukan Samar Da Ruwa

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kashe naira biliyan 1.116 domin gudanar da ayyukan samar da...

Labarai2 days ago

Sauye-sauyen Da Tinubu Ya Samar Ya Haifar Da Cigaba A Jihohi – Namadi

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan matakan da...

Labarai2 days ago

Jigawa Ta Yi Nazarin Sabbin Tsare-tsaren Masaukin Alhazai A Saudiyya

Daga Usman Muhammad Zaria Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ce tana nazarin hanyoyin inganta jin daɗin alhazai...

Labarai3 days ago

Kano: Kotu Ta Umarci A Lalata Buhunan Fulawa Sama Da 400

Daga Khadijah Aliyu  Wata kotu a Jihar Kano ta bayar da umarnin lalata buhunan fulawa sama da 400 da suka...

Labarai4 days ago

Tinubu Ya Jaddada Ƙudurin Samar Da Ci Gaba A Jigawa

Daga Usman Muhammad Zaria  Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sake jaddada ƙudurin gwamnatinsa na ci gaba da aiwatar da...

Labarai4 days ago

Shugaban Gidan Talabijin Na Katsina Abba Zayyan Ya Yi Murabus

Daga Isma’il Adamu  Babban Manajan gidan talabijin na Jihar Katsina (KTTV), Abba Zayyan, ya miƙa takardar murabus daga muƙaminsa a...

Labarai4 days ago

Namadi Ya Miƙa Buƙatu Uku Ga Tinubu Kan Ci gaban JiharJigawa

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya kai musu...

Mafi Shahara