Labarai
Tinubu Ya Jaddada Ƙudurin Samar Da Ci Gaba A Jigawa
Daga Usman Muhammad Zaria
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sake jaddada ƙudurin gwamnatinsa na ci gaba da aiwatar da sauye-sauye da hanzarta bunƙasa ƙasa, musamman a fannonin tsaro, tattalin arziki, ababen more rayuwa, noma, ilimi da inganta rayuwar al’umma.
Shugaban ya bayyana hakan ne a wajen gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC a Jihar Jigawa, inda ya buƙaci ‘yan Najeriya su kasance masu haɗin kai tare da goyon bayan manufofin gwamnatinsa. Ya ce za a ci gaba da aiwatar da shirye-shiryen samar da ayyukan yi, ƙarfafa tattalin arziki da inganta rayuwar al’umma.

Dangane da tsaro, Tinubu ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da ƙarfafa rundunonin sojoji da sauran hukumomin tsaro, ta hanyar samar musu da kayan aiki da inganta jin daɗinsu. Ya kuma yi alƙawarin inganta albashi da yanayin aikin jami’an tsaro bisa la’akari da irin sadaukarwar da suke yi wajen kare ƙasa.
A nasa jawabin, Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bayyana wasu ayyukan Gwamnatin Tarayya a Jigawa, ciki har da gina hanyoyi da gidaje ƙarƙashin shirin Renewed Hope da kuma shirin layin dogo da zai haɗa Najeriya da Maradi a Jamhuriyar Nijar. Ya kuma ambaci tallafin manoma, tare da kira ga al’ummar jihar su goyi bayan sake zaɓen Shugaba Tinubu.

Gwamnan Jihar Jigawa, Umar Namadi, ya yaba wa Shugaban Ƙasa bisa ayyukan raya ƙasa da ake gudanarwa a jihar, tare da tabbatar masa da goyon bayan al’ummar jihar.
Daraktan Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa, Sanata Abdulaziz Yari, ya ce ana ganin tasirin dimokuraɗiyya da sauye-sauyen gwamnatin Tinubu a faɗin ƙasar, musamman a Arewacin Najeriya. Shi ma Gwamnan Sokoto, Ahmed Aliyu, wanda ya yi magana a madadin gwamnonin APC, ya buƙaci al’ummar Jigawa su goyi bayan sake zaɓen Tinubu, yana mai danganta hakan da ayyukan raya ƙasa da ake gudanarwa a jihar. Ya kuma tuna da goyon bayan da Tinubu ya bai wa marigayi Muhammadu Buhari wajen kammala wa’adinsa na shekaru takwas.

Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Siyasa, Ibrahim Masari, ya ce halartar manyan shugabannin siyasar Arewa a gangamin na nuna goyon bayan yankin ga Shugaba Tinubu da kuma rawar da yake takawa a harkokin siyasar ƙasa.
A yayin taron, Shugaba Tinubu ya ƙaddamar da cibiyar koyon sana’o’i, taraktoci 300 da gwamnatin jihar ta samar, sai wasu 100 daga Gwamnatin Tarayya da injinan girbin amfanin gona guda 60.

Ya kuma ƙaddamar da hanyar da ta haɗa Tsohon Ofishin ‘Yan Sanda da Fadar Sarkin Dutse, inda ake sa ran ayyukan za su bunƙasa sana’o’i, inganta noma da sauƙaƙa zirga-zirga a jihar.
Fassara: Safiyah Abdulkadir
-
Labarai2 days agoJigawa Ta Amfana Da Ayyukan Gwamnatin Tinubu – Abdulaziz
-
Labarai4 days agoTsoffin Gwamnonin Jigawa Sun Yaba Wa Nasarorin Gwamna Namadi
-
Labarai4 days agoNamadi Ya Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen APC Na 2027
-
Labarai4 days agoYankin Funtua Sun Yi Fitowar Farin Dango A Yakin Neman Zaɓe Na APC- Hamza Faskari
-
Labarai3 days agoMajalisar Kano Za Ta Karɓi Kasafin Kuɗin Shekarar 2027
-
Labarai1 day agoNamadi Ya Miƙa Buƙatu Uku Ga Tinubu Kan Ci gaban JiharJigawa
-
Labarai2 days agoShettima Ya Bukaci ’Yan Najeriya Su Sake Zaben Tinubu A 2027
-
Labarai19 hours agoKano: Kotu Ta Umarci A Lalata Buhunan Fulawa Sama Da 400
