Labarai
Shettima Ya Bukaci ’Yan Najeriya Su Sake Zaben Tinubu A 2027
Daga Usman Muhammad Zaria
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bukaci ’yan Najeriya da su goyi bayan sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a babban zaɓen shekarar 2027, domin ba shi damar kammala ayyukan raya ƙasa da kuma ƙarfafa nasarorin da aka samu a ƙarƙashin shirin Renewed Hope.
Shettima ya yi wannan kira ne a wajen gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC da aka gudanar a filin wasa na Township da ke Dutse, Jihar Jigawa.
Ya ce gwamnatin Tinubu ta aza tubalin farfaɗo da tattalin arziki, bunƙasa ababen more rayuwa, ƙarfafa matasa da sauya fasalin harkokin noma a cikin shekaru uku da suka gabata, don haka akwai buƙatar ci gaba da tafiyar.
Ya bayyana cewa nasarorin da aka samu zuwa yanzu mafari ne na babban sauyi da ake son samu, yana mai cewa Shugaba Tinubu na buƙatar ƙarin lokaci domin kammala shirye-shiryensa na ci gaban ƙasa.
Shettima ya ce ayyuka masu muhimmanci da darajarsu ta kai biliyoyin Naira da aka ƙaddamar yayin ziyarar shugaban ƙasar, sun shaida ƙoƙarin gwamnatin APC na inganta rayuwar al’umma, samar da ayyukan yi da kuma bai wa matasa ƙwarewar sana’o’i.

Shettima ya yi nuni da irin goyon bayan da Tinubu ya bai wa shugabannin Arewa da suka zama shugabannin ƙasa a baya, yana mai bayyana hakan a matsayin hidima ta ƙashin kai ga Najeriya, tare da kira ga ‘yan Najeriya da su rama masa wannan alheri.
A yayin ziyarar aiki ta yini guda, Shugaba Tinubu ya ƙaddamar da wasu ayyuka da gwamnatin Jihar Jigawa ta aiwatar ƙarƙashin jagorancin Gwamna Umar Namadi, waɗanda suka haɗa da Cibiyar Renewed Hope Technical Services da ke Limawa, Dutse, wadda za ta samar da ayyukan ƙera kayayyakin masana’antu, walda da sauran tallafin fasaha.
Cibiyar za ta haɗa gwiwa da Cibiyar Horar da Sana’o’i ta Bola Ahmed Tinubu, wadda aka gina domin magance matsalar rashin aikin yi tsakanin matasa da bunƙasa masana’antu ta hanyar tsarin koyon ssana’o’i are da samun kuɗi daga aikin samar da kkayayyaki.Mataimakin Shugaban ƙasar ya kuma ƙaddamar da Cibiyar Fasaha da Ƙirƙire-Ƙirƙire ta Renewed Hope, wadda aka tsara domin bunƙasa ilimin fasahar zamani da ƙirƙire-ƙirƙire tsakanin matasan jihar.
A ɓangaren noma kuwa, Tinubu ya ƙaddamar da kayan aikin noma na zamani da gwamnatin jihar ta saya, waɗanda suka haɗa da taraktoci 400 tare da kayan aikinsu, injinan girbin amfanin gona 60, injinan shuka iri 150, injinan shuka shinkafa 150 da injinan feshin maganin kashe ƙwari 80.
Sauran ayyukan sun haɗa da babbar hanyar mota da ta tashi daga Garu zuwa fadar Sarkin Dutse, wadda ake sa ran za ta rage cunkoson ababen hawa tare da ƙawata babban birnin jihar.

Shettima ya yaba wa Gwamna Namadi bisa daidaita shirye-shiryen ci gaban jihar da manufofin Renewed Hope, ta hanyar zuba jari a fannin koyar da sana’o’i, noma na zamani da bunƙasa ababen more rayuwa.
Manyan baki da suka halarci gangamin sun haɗa da Shugaban Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas; gwamnonin jihohin Zamfara, Borno, Sokoto, Imo, Yobe, Kano da Kwara; mambobin Majalisar Tarayya; tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje; manyan jami’an gwamnati, jiga-jigan jam’iyyar da dubban magoya bayanta daga sassa daban-daban na ƙasar nan.
Fassara: Safiyah Abdulkadir
-
Labarai2 days agoJigawa Ta Amfana Da Ayyukan Gwamnatin Tinubu – Abdulaziz
-
Labarai4 days agoTsoffin Gwamnonin Jigawa Sun Yaba Wa Nasarorin Gwamna Namadi
-
Labarai4 days agoNamadi Ya Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen APC Na 2027
-
Labarai4 days agoYankin Funtua Sun Yi Fitowar Farin Dango A Yakin Neman Zaɓe Na APC- Hamza Faskari
-
Labarai1 day agoNamadi Ya Miƙa Buƙatu Uku Ga Tinubu Kan Ci gaban JiharJigawa
-
Labarai3 days agoMajalisar Kano Za Ta Karɓi Kasafin Kuɗin Shekarar 2027
-
Labarai19 hours agoKano: Kotu Ta Umarci A Lalata Buhunan Fulawa Sama Da 400
-
Labarai1 day agoArewa Za Ta Saka Wa Tinubu Da Ruwan Kuri’a A 2027- Yari
