Connect with us

Labarai

Jigawa Ta Amfana Da Ayyukan Gwamnatin Tinubu – Abdulaziz

Published

on

Daga Usman Muhammad Zaria

Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan harkokin yada labarai da wayar dan jama’a, Comrade Abdulaziz Abdulaziz, ya ce shugaban ya cika alkawuran da ya daukar wa al’ummar Jihar Jigawa, don haka ya cancanci sake zabensa a zaben 2027.

Abdulaziz ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai a Dutse, gabanin ziyarar da Shugaba Tinubu zai kai jihar a ranar Talata.

Ya ce Tinubu ya dade yana da kyakkyawar alaka da manyan jagororin siyasar Jigawa, tare da girmama su da daukacin al’ummar jihar. Yana mai cewa a ziyarar yakin neman zabensa a shekarar 2022, marigayi Sarkin Dutse, Alhaji Nuhu Muhammadu Sunusi, ya bukaci a kammala aikin samar da ruwan sha na Greater Dutse, wanda a yanzu ake ci gaba da gudanarwa.

Dangane da ayyukan more rayuwa, Abdulaziz ya ce gwamnatin tarayya na ci gaba da wasu ayyukan hanyoyi da aka gada daga gwamnatin baya, domin bunkasa zirga-zirgar jama’a da jigilar kayayyaki. Ya ce daga ciki akwai hanyar Kwanar Danja zuwa Tsalle zuwa Hadejia, wadda ta kai kashi 75 cikin 100, da hanyar  Kunya zuwa Kanya zuwa Babura, zuwa Babban Mutum, wadda ta kai kashi 82 cikin 100, da kuma hanyar  Kano zuwa Maiduguri, baya ga layukan dogo na Kano.zuwa Maradi da Kano zuwa Shuwarin.

Ya kuma lissafa ayyukan gidaje da suka hada da Renewed Hope Estates a Dutse da sauran kananan hukumomi, da gina gidaje 1,500 da ware filaye domin samar da gidaje masu saukin kudi.

A bangaren noma, ya ce daruruwan dubban manoma a Jigawa sun amfana da shirye-shiryen gwamnatin tarayya, wadanda suka hada da noman dabino a hekta 1,042, noman alkama a lokacin rani a hekta 120,000, aikin magudanan ruwa da ban-ruwa na Jahun, da raba kayan aikin gona na Naira biliyan biyar, baya ga tallafin kayan noma.

Dangane da tallafin jin kai, Abdulaziz ya ce shirin Renewed Hope Social Protection Scheme ya raba Naira biliyan 11 da rabi ga mutane sama da 178,000, yayin da shirin Renewed Hope Ward Development Programme ke tallafa wa iyalai masu karamin karfi ta hanyar tallafin kudi da sauran shirye-shiryen dogaro da kai.

Ya kara da cewa sama da dalibai miliyan daya a manyan makarantun gaba da sakandare a Arewacin Najeriya suna cin gajiyar shirin lamunin karatu na NELFUND, wanda ya rage wa iyaye nauyin kudin makaranta da sauran bukatun karatu.

Jami’in shugaban kasar ya kuma ce Shugaba Tinubu ya amince da kafa Jami’ar Noma a karamar hukumar Kirikasamma da Kwalejin Horar da ’Yan Sanda a Gwaram, baya ga samar da tashar wutar lantarki ta hasken rana mai darajar Naira biliyan daya a Jami’ar Tarayya ta Dutse.

Ya ce wadannan matakai na daga cikin kokarin gwamnati na inganta ilimi da samar da damar karatu ga yara, ba tare da la’akari da halin tattalin arzikin iyayensu ko yankin da suke zaune ba.

Abdulaziz ya bayyana cewa sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatin Tinubu ta bullo da su sun kara wa jihohi kudaden shiga, lamarin da ya taimaka wa Gwamna Umar Namadi wajen aiwatar da ayyukan raya kasa a Jigawa.

Ya yi kira ga al’ummar jihar da kada su yarda a yaudare su da alkawuran da ba su da tushe, inda ya bukace su da su sake zaben Shugaba Bola Ahmed Tinubu da sauran ‘yan takarar APC a zaben 2027, domin tabbatar da dorewar ayyukan raya kasa da samar da kyakkyawar makoma ga al’umma.

Fassara: Safiyah Abdulkadir

Labarai

Labarai19 hours ago

Kano: Kotu Ta Umarci A Lalata Buhunan Fulawa Sama Da 400

Daga Khadijah Aliyu  Wata kotu a Jihar Kano ta bayar da umarnin lalata buhunan fulawa sama da 400 da suka...

Labarai1 day ago

Tinubu Ya Jaddada Ƙudurin Samar Da Ci Gaba A Jigawa

Daga Usman Muhammad Zaria  Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sake jaddada ƙudurin gwamnatinsa na ci gaba da aiwatar da...

Labarai1 day ago

Shugaban Gidan Talabijin Na Katsina Abba Zayyan Ya Yi Murabus

Daga Isma’il Adamu  Babban Manajan gidan talabijin na Jihar Katsina (KTTV), Abba Zayyan, ya miƙa takardar murabus daga muƙaminsa a...

Labarai1 day ago

Namadi Ya Miƙa Buƙatu Uku Ga Tinubu Kan Ci gaban JiharJigawa

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya kai musu...

Labarai1 day ago

Arewa Za Ta Saka Wa Tinubu Da Ruwan Kuri’a A 2027- Yari

Daga Usman Muhammad Zaria  Daraktan Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na APC, Sanata Abdulaziz Yari, ya ce...

Labarai2 days ago

Shettima Ya Bukaci ’Yan Najeriya Su Sake Zaben Tinubu A 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bukaci ’yan Najeriya da su goyi bayan sake zaɓen Shugaba...

Labarai2 days ago

Jigawa Ta Amfana Da Ayyukan Gwamnatin Tinubu – Abdulaziz

Daga Usman Muhammad Zaria Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan harkokin yada labarai da wayar dan...

Labarai3 days ago

Majalisar Kano Za Ta Karɓi Kasafin Kuɗin Shekarar 2027

Daga Khadijah Aliyu  Majalisar Dokokin Jihar Kano na shirin karɓar daftarin kasafin kuɗin shekarar 2027 daga Gwamna Abba Kabir Yusuf...

Labarai4 days ago

Yankin Funtua Sun Yi Fitowar Farin Dango A Yakin Neman Zaɓe Na APC- Hamza Faskari

Daga Isma’il Adamu  An bayyana yakin neman zaben jam’iyyar APC a yankin Sanatan Funtua na Jihar Katsina a matsayin nasara,...

Labarai4 days ago

Namadi Ya Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen APC Na 2027

Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya ce an haɗa kwamitocin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa...

Mafi Shahara