Labarai
Yankin Funtua Sun Yi Fitowar Farin Dango A Yakin Neman Zaɓe Na APC- Hamza Faskari
Daga Isma’il Adamu
An bayyana yakin neman zaben jam’iyyar APC a yankin Sanatan Funtua na Jihar Katsina a matsayin nasara, wanda ke nuna yadda jam’iyyar ke samun karɓuwa a yankin.
Wani jigo a jam’iyyar kuma mai ruwa da tsaki a yankin, Hamza Suleiman Faskari, ya ce yakin neman zaben ya samu halartar dimbin magoya baya, an kuma gudanar da tarukan gangami cikin lumana, tare da tattaunawa da masu ruwa da tsaki a ƙananan hukumomi 11 na yankin.
A cewarsa, mata, matasa, manoma, ’yan kasuwa da ɗalibai sun fito ƙwarai domin tarbar Gwamna Dikko Radda da tawagarsa yayin ziyarar da suka kai ƙananan hukumomi da gundumomi daban-daban.
Hamza Faskari ya ce yawan jama’ar da suka fito ya nuna irin karɓuwar da APC ke da ita da kuma kwarin gwiwar samun nasara a zaɓen 2027.
Ya bayyana cewa yakin neman zaben bai tsaya ga harkokin siyasa kawai ba, domin Gwamnan ya kuma ƙaddamar da muhimman ayyukan raya ƙasa da aka aiwatar ƙarƙashin shirin gwamnatinsa na Building Your Future, tare da ƙaddamar da shirye-shiryen tallafa wa mata da matasa.
Ayyukan da aka ƙaddamar sun haɗa da tituna, cibiyoyin kiwon lafiya matakin farko da aka inganta, gyaran makarantu da shirye-shiryen tallafa wa harkokin noma.
Haka kuma, shirye-shiryen tallafin sun haɗa da ba da tallafin kuɗi ga mata ’yan kasuwa, kayan sana’o’i ga masu sana’o’in hannu da kayan tallafa wa manoma.
Hamza Faskari, wanda shi ne Kwamishinan Muhalli na Jihar Katsina kuma ɗan takarar APC mai wakiltar mazabar tarayya ta Kankara/Sabuwa/Faskari, ya ƙara da cewa Gwamnan ya gudanar da taron tattaunawa da sarakuna, shugabannin addinai, ’yan kasuwa da masu ruwa da tsaki a siyasa.
Da yake jawabi a wajen tarukan gangamin, Gwamna Radda ya ce gwamnatinsa ta cika alkawuran da ta ɗauka a lokacin yaƙin neman zaɓe, tare da aiwatar da wasu ayyuka bisa buƙatun al’ummomin da ke cikin mazabu 361 na jihar.
Gwamnan, wanda shi ne kodinetan kwamitin kamfen na Tinubu-Dikko a jihar Katsina, ya buƙaci mambobin APC su ba da muhimmanci ga haɗin kai, sulhu da wayar da kan jama’a tun daga gundumomi zuwa matakin jiha.
Ya ce muhimman abubuwan da gwamnatinsa ta sa gaba sun haɗa da tsaro, ababen more rayuwa, ilimi, kiwon lafiya da samar da damarmakin tattalin arziki, inda ya buƙaci al’umma su mara wa Shugaba Bola Tinubu da sauran ’yan takarar APC baya a zaɓen 2027.
Da yake jawabi a wajen gangamin da aka gudanar a Matazu, Radda ya bayyana tarbar da suka samu a yankin Funtua a matsayin wata alama ta ƙwarin gwiwar da jam’iyyar ke da shi a matakin ƙasa, tare da nuna kyakkyawan fata na samun nasara a zaɓen 2027.
Ana sa ran tawagar yakin neman zaben na Tinubu-Dikko za ta kai irin wannan ziyara yankunan Sanatocin Daura da Katsina a makonni masu zuwa.
Fassara: Safiyah Abdulkadir
-
Labarai2 days agoJigawa Ta Amfana Da Ayyukan Gwamnatin Tinubu – Abdulaziz
-
Labarai4 days agoTsoffin Gwamnonin Jigawa Sun Yaba Wa Nasarorin Gwamna Namadi
-
Labarai4 days agoNamadi Ya Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen APC Na 2027
-
Labarai3 days agoMajalisar Kano Za Ta Karɓi Kasafin Kuɗin Shekarar 2027
-
Labarai1 day agoNamadi Ya Miƙa Buƙatu Uku Ga Tinubu Kan Ci gaban JiharJigawa
-
Labarai2 days agoShettima Ya Bukaci ’Yan Najeriya Su Sake Zaben Tinubu A 2027
-
Labarai19 hours agoKano: Kotu Ta Umarci A Lalata Buhunan Fulawa Sama Da 400
-
Labarai1 day agoArewa Za Ta Saka Wa Tinubu Da Ruwan Kuri’a A 2027- Yari
