Labarai
Mutane Aƙalla 64 Sun Mutu a Haɗarin Jiragen Ƙasa a Sifaniya
Mutane aƙalla 64 sun mutu bayan wasu jiragen ƙasa guda biyu masu saurin gudu sun yi karo da juna a tsakiyar ƙasar Sifaniya, yayin da ake fargabar adadin waɗanda suka mutu zai ƙaru.
Hatsarin ya faru ne a safiyar Laraba, 28 ga Oktoban 2026, a layin dogo da ya haɗa birnin Madrid da Seville, kusa da garin Urda da ke yankin Toledo.
Rahotanni sun ce jiragen ƙasan da suka yi karo sun haɗa da na kamfanonin Renfe da Iryo, waɗanda ke tafiya daga Madrid zuwa Seville.
Bayanai na farko sun nuna cewa jirgin ƙasan Renfe ya bugi bayan jirgin Iryo, lamarin da ya sa wasu daga cikin taragon jiragen suka fita daga kan layin dogo, inda wasu suka gangara zuwa wani gangare.
Jiragen biyu na ɗauke da fasinjoji sama da 500. Jirgin Iryo na ɗauke da fasinjoji 147, ciki har da jariri, yayin da jirgin Renfe ke ɗauke da fasinjoji 397.
Ma’aikatan agajin gaggawa, jami’an ‘yan sanda, masu kashe gobara da jami’an lafiya sun isa wurin domin ceto waɗanda suka tsira da kuma kai waɗanda suka jikkata asibitoci.
Hukumomin Sifaniya sun dakatar da zirga-zirgar jiragen ƙasa a kan hanyar Madrid zuwa yankin Andalusia, yayin da ake ci gaba da aikin ceto da bincike domin gano musabbabin hatsarin.
-
Labarai4 days agoRundunar ‘Yan Sanda Ta Tabbatar da Rasuwar Sheikh Yahaya Masussuka
-
Labarai3 days agoSu Waye Suka Kashe Sheikh Yahaya Masussuka a Dutsin-Ma
-
Labarai3 days agoBa Za a Amince da Raba Kafa a Zabukan 2027 Ba — Ministan Yada Labarai
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Tabbatar Da Nadin Kwamishinoni Shida
-
Kasuwanci3 days agoTsohon Ministan Harkokin Waje Gambari Ya Ƙalubalanci Matasa Kan Zaman Lafiya Da Gina Ƙasa
-
Kasuwanci3 days agoNijeriya Za Ta Fara Kera Makamai Da Kayayyakin Tsaro Masu Yawa
-
Labarai2 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Amince da Kudirin Kafa ’Yan Sandan Jiha
-
Labarai2 days agoKatsina: Dalibai 64 Sun Jikkata Bayan An Musu Rigakafin Cutar Tsargiya
