Labarai
Majalisar Dokokin Kano Ta Amince da Kudirin Kafa ’Yan Sandan Jiha
Daga Khadijah Aliyu
Majalisar Dokokin Jihar Kano ta amince da wani kudiri da ke neman yin gyara ga Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya na shekarar 1999, domin samar da damar kafa rundunar ’yan sandan jiha.
An amince da kudirin ne a zaman majalisar da Kakakinta, Jibril Ismail-Falgore, ya jagoranta.
Shugaban majalisar ya ce ’yan majalisar sun yi nazari tare da amincewa da kudirin bayan tattauna sassa na ɗaya zuwa na 26 a zaman majalisar.
Ya bayyana cewa amincewa da kudirin ya yi daidai da ikon da sashe na 9(2) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na shekarar 1999 ya bai wa majalisar.
Kudirin na neman yin gyara ga kundin tsarin mulkin domin samar da tsarin doka da zai ba da damar kafa rundunar ’yan sandan jiha, tare da tanade-tanaden da suka shafi hakan.
KHADIJAH ALIYU
-
Labarai4 days agoRundunar ‘Yan Sanda Ta Tabbatar da Rasuwar Sheikh Yahaya Masussuka
-
Labarai3 days agoSu Waye Suka Kashe Sheikh Yahaya Masussuka a Dutsin-Ma
-
Labarai3 days agoBa Za a Amince da Raba Kafa a Zabukan 2027 Ba — Ministan Yada Labarai
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Tabbatar Da Nadin Kwamishinoni Shida
-
Kasuwanci3 days agoTsohon Ministan Harkokin Waje Gambari Ya Ƙalubalanci Matasa Kan Zaman Lafiya Da Gina Ƙasa
-
Kasuwanci3 days agoNijeriya Za Ta Fara Kera Makamai Da Kayayyakin Tsaro Masu Yawa
-
Labarai2 days agoMutane Aƙalla 64 Sun Mutu a Haɗarin Jiragen Ƙasa a Sifaniya
-
Labarai2 days agoKatsina: Dalibai 64 Sun Jikkata Bayan An Musu Rigakafin Cutar Tsargiya
