Connect with us

Kasuwanci

Tsohon Ministan Harkokin Waje Gambari Ya Ƙalubalanci Matasa Kan Zaman Lafiya Da Gina Ƙasa

Published

on

Daga ALI MUHAMMAD RABIU

Tsohon Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Farfesa Ibrahim Gambari, ya yi kira ga matasan ƙasar da su rungumi tattaunawa, riƙon amana da shugabanci na gari domin magance ƙalubalen ƙasa da bunƙasa ci gaba mai ɗorewa.

Gambari ya ce Najeriya na buƙatar matasa masu iya warware saɓani cikin lumana, samar da sabbin dabaru da kuma fifita muradun al’umma a kan burin kansu.

Ya bayyana hakan ne a cikin saƙon fatan alheri da godiya da aka gabatar a madadinsa a Jami’ar Ilorin da ke Jihar Kwara, inda Cibiyar Nazarin Zaman Lafiya da Tsare-tsare da Ƙungiyar Ɗaliban Nazarin Zaman Lafiya da Tsare-tsare suka karrama shi da lambar yabo ta Golden Olive Award.

Da yake jawabi ta hannun Kanar Ademola Lawal mai murabus, Farfesa Gambari ya ce makomar ƙasar ba ta dogara da takardun shaidar karatun matasa kaɗai ba, har ma da ɗabi’unsu, riƙon amana da jajircewarsu wajen yi wa al’umma hidima.

Ya buƙaci matasan Najeriya da su fahimci cewa shugabanci ba ya taƙaita ga samun muƙami ko sarauta, sai dai ya ta’allaka ne da niyyar yi wa al’umma hidima da bayar da gudummawa ga ci gabanta.

Da yake waiwayar rayuwarsa daga Bode Saadu da Malete a Jihar Kwara zuwa fagen diflomasiyya na ƙasa da ƙasa, Gambari ya buƙaci ɗalibai da kada su bari asalin inda suka fito ya zama shinge ga burinsu na cimma nasara.

Sai dai ya jaddada cewa dole ne a haɗa buri da ƙwarewa, kyawawan ɗabi’u da shiri mai kyau domin cin gajiyar damarmakin da ake samu.

Tsohon ministan ya kuma nuna muhimmancin zuba jari a fannin ilimi, bincike da horas da mutanen da za su jagoranci ayyukan samar da zaman lafiya a nan gaba.

Ya gode wa shugabancin jami’ar, malamai da ɗaliban ƙungiyar bisa karramawar, yana mai bayyana ta a matsayin wata gagarumar shaida ta doguwar alaƙarsa da Jihar Kwara.

Fassara: Shafii Abubakar Wababe 

Labarai

Labarai2 days ago

Mutane Aƙalla 64 Sun Mutu a Haɗarin Jiragen Ƙasa a Sifaniya

Mutane aƙalla 64 sun mutu bayan wasu jiragen ƙasa guda biyu masu saurin gudu sun yi karo da juna a...

Labarai2 days ago

Katsina: Dalibai 64 Sun Jikkata Bayan An Musu Rigakafin Cutar Tsargiya

Daga Isma’il Adamu  Aƙalla dalibai 64 na makarantar sakandaren kimiyya ta gwamnati da ke Batagarawa, a jihar Katsina, aka garzaya...

Labarai2 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Amince da Kudirin Kafa ’Yan Sandan Jiha

Daga Khadijah Aliyu Majalisar Dokokin Jihar Kano ta amince da wani kudiri da ke neman yin gyara ga Kundin Tsarin...

Kasuwanci3 days ago

Nijeriya Za Ta Fara Kera Makamai Da Kayayyakin Tsaro Masu Yawa

Daga Shindong Bala, Kaduna Nijeriya za ta fara kera makamai da sauran kayayyakin tsaro , domin amfanin ƙasar da kuma...

Kasuwanci3 days ago

Tsohon Ministan Harkokin Waje Gambari Ya Ƙalubalanci Matasa Kan Zaman Lafiya Da Gina Ƙasa

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Tsohon Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Farfesa Ibrahim Gambari, ya yi kira ga matasan ƙasar da su...

Labarai3 days ago

Ba Za a Amince da Raba Kafa a Zabukan 2027 Ba — Ministan Yada Labarai

Daga Aliyu Lawal, Minna Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al’umma, Mohammed Idris, ya buƙaci mambobin jam’iyyar APC da...

Labarai3 days ago

Su Waye Suka Kashe Sheikh Yahaya Masussuka a Dutsin-Ma

Wasu ’yan bindiga da ake zargi da aikata laifuka sun kashe fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Yahaya Masussuka, a gidansa...

Labarai4 days ago

Rundunar ‘Yan Sanda Ta Tabbatar da Rasuwar Sheikh Yahaya Masussuka

Daga Isma’il Adamu Rundunar ’yan sandan jihar Katsina ta tabbatar da kashe fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Yahaya Masussuka, da...

Labarai4 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Tabbatar Da Nadin Kwamishinoni Shida

Daga Khadijah Aliyu Majalisar Dokokin Jihar Kano ta tantance tare da tabbatar da naɗin mutane shida da aka gabatar domin...

Ilimi1 week ago

KANO: Ungogo Ta Ƙaddamar da Shirin Shigar da Yara Makaranta

Daga Khadijah Aliyu Ƙaramar Hukumar Ungogo ta Jihar Kano ta ƙaddamar da wani shirin wayar da kan jama’a domin shigar...

Mafi Shahara