Labarai
Majalisar Dokokin Kano Ta Tabbatar Da Nadin Kwamishinoni Shida
Daga Khadijah Aliyu
Majalisar Dokokin Jihar Kano ta tantance tare da tabbatar da naɗin mutane shida da aka gabatar domin zama kwamishinoni a Majalisar Zartarwar Jihar.
An gudanar da tantancewar ne yayin zaman majalisar ƙarƙashin jagorancin shugabnta, Jibril Ismail Falgore.
Tantancewar ta biyo bayan wani ƙuduri da Shugaban Masu Rinjaye, Lawan Hussaini, ya gabatar, wanda Shugaban Marasa Rinjaye, Usman Abubakar, ya mara wa baya, domin neman amincewar majalisar ta tantance tare da tabbatar da naɗin mutanen.
Da yake jawabi yayin zaman, Shugaban Masu Rinjaye ya bayyana cewa waɗanda aka tantance sun cika dukkan sharuɗɗan da ake buƙata domin naɗa su kwamishinoni a Majalisar Zartarwar Jihar.
Ya ce majalisar ta gamsu da ƙwarewa da gogewar waɗanda aka tantance, inda ya bayyana cewa wasu daga cikinsu sun taɓa riƙe muƙaman kwamishinoni, yayin da wasu suka riƙe muƙamai kamar shugabancin Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Jihar Kano (KANSIEC) da sauran muƙaman gwamnati.

Majalisar Dokokin Kano Ta Tabbatar da Kwamishinoni ShidaMajalisar Dokokin Kano Ta Tabbatar da Kwamishinoni Shida
Lawan Hussaini ya ƙara da cewa za a sanar da bangaren zartarwa game da tabbatar da naɗin domin a raba wa sababbin kwamishinonin muƙaman da za su riƙa jagoranta.
Da yake nasa jawabin bayan tantancewar, tsohon shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Jihar Kano, Farfesa Sani Lawan Malumfashi, ya jaddada muhimmancin bunƙasa ilimin kimiyya da fasaha, ƙirƙire-ƙirƙire da harkokin kasuwanci domin bai wa al’umma ƙwarewar da za ta taimaka musu wajen dogaro da kansu.
Shi ma wani daga cikin waɗanda aka tantance, tsohon Kwamishinan Lafiya da Muhalli, Aminu Ibrahim Tsanyawa, ya yi alƙawarin yin aiki tukuru domin bunƙasa Jihar Kano da inganta jin daɗin mazaunanta.
Sauran waɗanda aka tantance da suka yi jawabi sun haɗa da mai ritaya Air Commodore Salisu Yusha’u, Mukhtari Ishaq, Ibrahim Namadi da Idris Garba.
Sun bayyana aniyarsu ta bayar da gudummawa wajen ci gaban jihar da kuma inganta rayuwar al’ummarta.
Fassara: Safiyah Abdulkadir
-
Labarai4 days agoRundunar ‘Yan Sanda Ta Tabbatar da Rasuwar Sheikh Yahaya Masussuka
-
Labarai3 days agoSu Waye Suka Kashe Sheikh Yahaya Masussuka a Dutsin-Ma
-
Labarai3 days agoBa Za a Amince da Raba Kafa a Zabukan 2027 Ba — Ministan Yada Labarai
-
Kasuwanci3 days agoTsohon Ministan Harkokin Waje Gambari Ya Ƙalubalanci Matasa Kan Zaman Lafiya Da Gina Ƙasa
-
Kasuwanci3 days agoNijeriya Za Ta Fara Kera Makamai Da Kayayyakin Tsaro Masu Yawa
-
Labarai2 days agoMutane Aƙalla 64 Sun Mutu a Haɗarin Jiragen Ƙasa a Sifaniya
-
Labarai2 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Amince da Kudirin Kafa ’Yan Sandan Jiha
-
Labarai2 days agoKatsina: Dalibai 64 Sun Jikkata Bayan An Musu Rigakafin Cutar Tsargiya
