Labarai
Gwamnatin Jigawa Za Ta Kafa Cibiyar Ayyukan Noma Da Samar Sa Kayayyakin Zamani
Daga Usman Muhammad Zaria
Majalisar Zartarwar Jihar Jigawa ta amince da sakin Naira Biliyan 7.4 domin biyan ragowar kuɗaɗen kayan aikin noma da kuma kafa Cibiyar Ayyukan Noma, ƙarƙashin shirin Gwamnatin Tarayya na Renewed Hope National Agricultural Mechanisation Programme (RH-NAMP).
Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai bayan taron majalisar da aka gudanar a Gidan Gwamnati da ke Dutse.
Ya ce amincewar za ta ƙarfafa aikin noma da injuna, da inganta damar manoma ta samun kayan aikin zamani da ayyukan tallafi.
Sagir Musa ya ce samar da kayan aikin zai ƙara wa manoma damar yin amfani da injuna wajen shirya gona da noma, inganta aiki, rage dogaro da aikin hannu, tare da ƙara yawan amfanin gona a jihar.
Kwamishinan ya ƙara da cewa majalisar ta amince da kafa cibiyar haɗa ayyukan tallafa wa noma, ciki har da samar da kayan aikin noma, horar da manoma, gyaran injuna, tattara amfanin gona da ayyukan bayan girbi.
Ya ce cibiyar za ta samar da dandali na bai wa manoma da sauran masu ruwa da tsaki a harkar noma damar samun ayyukan noma da injuna, tare da samar da wurin ajiya, kula da gyara taraktoci da sauran kayan aikin noma.
Fassara: Safiyah Abdulkadir
-
Labarai4 days agoHukumar Alhazai Ta Jigawa Ta Bayyana Alhininta Bisa Rasuwar Suleiman Usman
-
Fasaha3 days agoNASENI Ta Ƙarfafa Horar da Sana’o’i da Fasahar Jiragen Sama Marasa Matuki a Kaduna
-
Labarai3 days agoNSCDC Ta Kama Wanda Ake Zargi Da Safarar Mutane A Zamfara
-
Labarai2 days agoGwamna Uba Sani Ya Ce Bunƙasa Ƙwarewa Na Da Muhimmanci Ga Farfaɗo Da Tattalin Arziki
-
Labarai2 days agoGwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya
-
Labarai2 days agoGwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga
-
Labarai2 days agoTajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14
-
Labarai2 days ago’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano
