Labarai
Dan Majalisar Dawakin Kudu Ya Yi Alkawarin Ingantaccen Wakilci Da Ci gaban Karkara
Daga Khadijah Aliyu,Kano
Sabon ɗan majalisar da ke wakiltar mazabar Dawakin Kudu a Majalisar Dokokin Jihar Kano, Yusuf Datti Hussaini, ya yi alkawarin samar da ingantaccen wakilci a majalisa da kuma inganta ci gaban al’umma ta hanyar manufofi masu amfani ga jama’a da ayyukan raya ƙasa masu ma’ana.
Datti ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a harabar Majalisar Dokokin Jihar Kano, jim kaɗan bayan rantsar da shi. Ya tabbatar wa al’ummar mazabarsa cewa zai mai da hankali wajen samar da dokoki da za su inganta rayuwarsu.
Ɗan majalisar ya ce ajandar majalisarsa za ta fi mayar da hankali ne kan gabatar da ƙudure-ƙudure da kuma ƙirƙirar dokoki da za su magance buƙatun ci gaban mazabar Dawakin Kudu, tare da tabbatar da cewa ci gaban ya dace da ƙa’idojin da ake amfani da su a duniya.
Ya kuma yi alkawarin yin aiki tukuru domin tabbatar da aiwatar da muhimman ayyuka da shirye-shiryen da Majalisar Dokokin Jihar ta amince da su.
Datti ya ce magance matsalolin ci gaban da ke fuskantar mazabar Dawakin Kudu na buƙatar kyakkyawan tsari da ingantattun dokoki da kuma jajircewa wajen aiwatar da ayyuka da shirye-shiryen da za su inganta rayuwar mazauna yankin tare da samar musu da fa’ida kai tsaye a matakin ƙasa.
Ɗan majalisar ya kuma yi kira ga al’ummar mazabarsa da su kasance masu sa ido da kuma shiga cikin harkokin majalisa, ta hanyar bibiyar ƙudure-ƙudure da dokokin da ake gabatarwa da kuma waɗanda Majalisar ta amince da su.
Ya jaddada muhimmancin sa hannun jama’a da yin hulɗa mai ma’ana wajen inganta gaskiya da rikon amana, tare da tabbatar da cewa ayyukan majalisa sun haifar da ci gaba mai ma’ana a faɗin mazabar.
Alƙawarin sabon ɗan majalisar na samar da ingantaccen wakilci na zuwa ne a daidai lokacin da al’ummar Dawakin Kudu ke sa ran samun sabuwar himma wajen wakilci da kuma aiwatar da shirye-shiryen ci gaba a yankin.
Datti ya sake jaddada aniyarsa ta yin aiki don inganta jin daɗin al’ummar mazabarsa ta hanyar samar da ingantattun dokoki da ɗaukar matakan da suka dace da kuma haɗin gwiwa da hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki.
Zuwan Datti a Majalisar Dokokin Jihar Kano ta biyo bayan zaɓen cike gurbi da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta gudanar a ƙaramar hukumar Dawakin Kudu ta Jihar Kano, inda ya tsaya takara ƙarƙashin jam’iyyar APC.
Daga bisani, Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano, Jibril Isma’il Falgore, ya rantsar da shi a matsayin ɗan majalisa yayin zaman majalisar.
Fassara: Shafii Abubakar Wababe
-
Labarai4 days agoHukumar Alhazai Ta Jigawa Ta Bayyana Alhininta Bisa Rasuwar Suleiman Usman
-
Fasaha3 days agoNASENI Ta Ƙarfafa Horar da Sana’o’i da Fasahar Jiragen Sama Marasa Matuki a Kaduna
-
Labarai3 days agoNSCDC Ta Kama Wanda Ake Zargi Da Safarar Mutane A Zamfara
-
Labarai2 days agoGwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya
-
Labarai2 days agoGwamna Uba Sani Ya Ce Bunƙasa Ƙwarewa Na Da Muhimmanci Ga Farfaɗo Da Tattalin Arziki
-
Labarai2 days agoGwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga
-
Labarai2 days agoTajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14
-
Labarai2 days ago’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano
