Connect with us

Labarai

Hukumar Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa Ta Kai Samame Gidan Kakakin Majalisar Afrika Ta Kudu

Published

on

Masu bincike sun kai samame gidan shugabar majalisar dokokin kasar Afrika ta Kudu, bisa zargin da ake mata na cin hanci da rashawa, wanda hakan ya sanya ‘yan adawa suka bukaci ta yi murabus.

Hakan dai na zuwa ne watanni biyu kafin babban zaben kasar, a dai-dai lokacin da ake ci gaba da kai wa ‘ya’yan jam’iyar da ke mulki ta ANC samame, bisa zarginsu da aikata badakalar cin hanci da rashawa.

 

Hukumar da ke yaki da cin hancin da rashawa ta kasar dai ta tabbatar da cewa, wata babbar tawagar jami’anta sun kai samamen ne don gudanar da binciken a gidan shugabar majalisar Nosiviwe Mapisa-Nqakula da ke Johannesburg.

 

Majalisar dokokin kasar dai ta ce wannan binciken da ake yi wa Mapisa-Nqakula, na da alaka da zargin badakala da ake mata lokacin ta na ministar tsaron kasar.

 

Mapisa-Nqakula ta rike mukamin ministar tsoron kasar ne tsakanin shekarar 2014 zuwa 2021, kafin daga bisani aka nadata kakakin majalisar dokokin kasar, da hakan ya fuskanci suka daga bangaren ‘yan adawa.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai

Labarai20 hours ago

Amurka Ta Dakatar Da Kudurin Kai Jirgin Bama-Bamai Zuwa Isra’ila

Amurka ta sanar da batun dakatar da shirin ta na kai jirgi dauke da bamabamai zuwa Israila a cikin makon...

Labarai20 hours ago

NAHCON Ta Jinjinawa Hukumar Alhazai Ta Jihar Jigawa Bisa Shirye-shiryen Hajjin Bana

Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa Alhaji Ahmed Umar Labbo ya karbi tawagar gani da ido...

Kasuwanci2 days ago

CBN Ya Bai Wa Masu POS Wa’adin Yin Rajista Da Gwamnati

Babban Bankin Najeriya CBN ya bayar da wa’adin ranar 7 ga watan  Yulin 2024 ga masu POS su kammala rajista...

Fasaha2 days ago

Kusan Malaman Makaranta Dubu 2 Ke Samun Horo a Barno

  Gwamnatin jihar Borno ta fara aikin horas da malamai 1,949 a matakin farko da aka gano cewa suna iya...

Fasaha2 days ago

Bankuna Za Su Fara Cirar 0.5% Daga Masu Tura Kudi Ta Intanet

  Babban Bankin Najeriya (CBN) ya umurci bankunan kasar su fara cirar kaso 0.5 cikin 100 na duk kuɗin da...

Labarai2 days ago

An kashe Falasɗinawa 34,800 tun fara yaƙi – Ma’aikatar lafiyar Hamas

Ma’aikatar lafiya ta Hamas a Gaza ta ce an kashe Falasdinawa 34,789 a yankin tun ranar 7 ga watan Oktoba,...

Ilimi5 days ago

Gwamnatin Jigawa Za Ta Samar Da Gidaje A Jami’ar Tarayya Da Ke Babura

Gwamnatin jihar Jigawa ta ce za ta ci gaba da tallafawa harkokin koyo da koyarwa a Jami’ar Fasaha ta Gwamnatin...

Labarai5 days ago

An Samar Da Sabon Tsari Da Zai Inganta Harkar Noman Rogo A Najeriya

Shugaban kungiyar masu noman rogo ta Najeriya (NCGA), Mustapha Othman Bakano, ya kaddamar da wani tsari na samar da kasuwa...

Labarai7 days ago

Gwamnatin Jigawa Za Ta Samar Da Tarakta 300 Ga Manoma Daga Amurka

A kokarinta na ci gaba da habbaka harkokin noma, Gwamnatin Jihar Jigawa ta ƙulla wata yarjejeniyar haɗin gwiwa da wasu...

Labarai7 days ago

An kama masu zanga-zanga 17 a jami’ar Texas

An sake kama ƙarin mutanen da ke da alaƙa da zanga-zangar nuna goyon baya ga Falasɗinawa inda a wannan karon...

Mafi Shahara