Kasuwanci
Gwamnatin Jigawa Ta Amince da Sakin Kuɗaɗe Domin Gudanar da Taron Zuba Jari na 2026
Daga Usman Muhammad Zaria
Gwamnatin Jihar Jigawa ta ce ta amince da sakin kuɗaɗen da aka riga aka ware wa Hukumar Kula da Hannayen Jari ta jihar, wato Jigawa Invest, domin gudanar da Taron Zuba Jari na Jihar Jigawa na shekarar 2026, a wani mataki da ya yi daidai da ƙudirin gwamnatin mai ci na bunƙasa tattalin arziki, jawo masu zuba jari, samar da ayyukan yi da kuma inganta ci gaba mai ɗorewa a faɗin jihar.
Kwamishinan Yaɗa Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed ne ya bayyana hakan jim kaɗan bayan kammala taron Majalisar Zartarwa ta Jiha da aka gudanar a Fadar Gwamnati da ke Dutse.
Ya bayyana cewa, ana sa ran Taron Zuba Jari na Jigawa na shekarar 2026 zai kasance babban dandali na haɗa masu zuba jari na cikin gida da na ƙasashen waje, abokan hulɗar ci gaba, cibiyoyin kuɗi, shugabannin kasuwanci da masu tsara manufofi domin tattauna damar zuba jari da ke akwai a jihar.
A cewarsa, taron zai nuna irin ƙarfin tattalin arzikin Jigawa, fa’idodinta na musamman da kuma muhimman fannoni da ake son a zuba jari a cikinsu, da suka haɗa da noma, sarrafa kayayyakin amfanin gona, makamashi, masana’antu, ma’adinai, kasuwanci, ababen more rayuwa da fasaha.
Kwamishinan ya ƙara da cewa amincewar majalisar na gudanar da taron ya yi daidai da babban shirin tattalin arzikin gwamnatin jihar na inganta yanayin kasuwanci, ƙarfafa haɗin gwiwar gwamnati da masu zaman kansu, da kuma amfani da dimbin damar tattalin arziki da ke faɗin jihar.
Alhaji Sagir Musa Ahmed ya kuma bayyana cewa kuɗaɗen da aka amince da sakin su za su taimaka wajen shiryawa da gudanar da taron, aiwatar da tattaunawa da masu ruwa da tsaki, yaɗa damar zuba jari, kammala shirye-shiryen fasaha da sauran ayyukan da za su tabbatar da nasarar taron tare da samar da sakamako mai anfani ga tattalin arzikin jihar.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
