Labarai
Uwargidan Shugaban Kasa Ta Ƙaddamar da Shirin Abinci a Arewa Maso Gabas
Uwargidan Shugaban Kasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta ƙaddamar da shirin samarda Abinci na Ƙasa a yankin Arewa maso Gabas, domin magance matsalar ƙarancin abinci mai gina jiki ga yara a ƙasar nan.
An ƙaddamar da shirin ne a Maiduguri, Jihar Borno, inda ta bayyana cewa matsalar tamowa a tsakanin yara babbar barazana ce da ke buƙatar daukin gaggawa.
Ta ce an tsara shirin ne domin samar da abinci mai gina jiki ga masu buƙata musamman mata masu juna biyu, masu shayarwa da kuma yara masu shekaru tsakanin haihuwa zuwa shida.
Sanata Oluremi Tinubu ta bayyana cewa har yanzu miliyoyin yara a Najeriya ba sa samun isasshen abinci mai gina jiki, saboda haka gwamnati ke faɗaɗa shirin zuwa sassan ƙasar domin kai tallafi ga masu buƙata.
Ta kuma buƙaci haɗin gwiwa tsakanin gwamnati, kamfanoni masu zaman kansu da al’umma domin tabbatar da dorewar shirin.
Uwargidan shugaban ƙasar ta ce wannan shiri na cikin manufofin “Renewed Hope Agenda” na Shugaba Bola Tinubu, musamman a ɓangarorin samar da wadataccen abinci da inganta lafiya.
A nasa jawabin, Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya yabawa gwamnatin tarayya bisa ci gaba da tallafawa jihar, musamman wajen shawo kan matsalolin da tashe-tashen hankula suka haifar.
Shi ma Ministan Lafiya da Jin Daɗin Al’umma, Farfesa Mohammed Ali Pate, ya ce za a kafa bankunan abinci a matakin ƙananan hukumomi, inda za a riƙa bai wa masu buƙata takardun karɓar abinci mai gina jiki ta cibiyoyin lafiya.
Ministan Noma, Sanata Abubakar Kyari, ya ce shirin zai taimaka wajen tabbatar da cewa mata da yara masu fama da tamowa sun samu tallafin abinci yadda ya dace.
Baya ga haka, Uwargidan Shugaban Ƙasar ta kuma ƙaddamar da gidajen ma’aikatan jinya, da wasu makarantu na firamare da sakandare a jihar, tare da ganawa da Shehun Borno da sauran sarakunan gargajiya.
Bello Wakili/Abuja
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
