Connect with us

Kasuwanci

EFS Ta Tallafa wa Zawarawa Da Masu Karamin Karfi Sama Da 100 A Taraba

Published

on

Wata cibiyar kasuwanci ta yanar gizo da ke da hedikwata a Amurka, mai suna EFS, ta tallafa wa sama da zawarawa da masu ƙaramin ƙarfi 100 a yankin Shavoh da ke ƙaramar hukumar Jalingo a jihar Taraba, inda ta raba musu kayan masarufi a taron agajinta na biyu da aka gudanar a Jalingo.

Mai kula da harkokin EFS a jihar, Ambassador Boniface Koson, ya ce cibiyar ce ta ɗauki nauyin shirin gaba ɗaya a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarinta na ayyukan jin ƙai da bunƙasa al’umma.

Ya bayyana cewa an zaɓi waɗanda suka ci gajiyar tallafin ne ta hanyar haɗin gwiwar membobin EFS da coci-coci da masallatai da kuma al’ummar yankin, domin tabbatar da cewa tallafin ya isa ga masu buƙata na gaskiya.

Koson ya ƙara da cewa an kafa EFS a Amurka a shekarar 2019, sannan ta fara aiki a Nigeria a 2023, kuma an yi mata rajista a hukumomin kula da kamfanonin ta Kasa (CAC) da kuma hukumar yaki da safarar kudade ba bisa ka’ida ba (Special Control Unit against Money Laundering) a watan Janairun 2026.

Ya ce wannan shiri ya nuna cewa EFS ba wai tana mayar da hankali ne kawai kan bunƙasa tattalin arziki ba, har ma tana da burin inganta rayuwar al’umma ta hanyar tallafi kai tsaye.

A yayin shirin, an raba kayan masarufi kamar su kayan yaji, sabulu, taliya da gishiri ga waɗanda suka amfana, a wani yunƙuri na tallafa wa marasa galihu a cikin al’umma.

Jamila Abba/Jalingo

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai7 days ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara