Connect with us

Labarai

FRCN Ta Cika Shekaru 75, Ta Jaddada Ƙarfafa Haɗin Kan Ƙasa

Published

on

Darakta Janar na Radio Nijeriya FRCN, Dr Mohammed Bulama, ya bayyana cewa gidan rediyon zai ci gaba da zama wata muhimmiyar murya wajen haɗa kan al’ummar Najeriya da kuma tallafa wa ci gaban ƙasa, yayin bikin cika shekaru 75 da kafuwarsa a Abuja.

Da yake jawabi a wajen bikin, Dr Bulama ya gode wa Allah Maɗaukakin Sarki tare da nuna jin daɗinsa ga Gwamnatin Tarayya da al’ummar Najeriya bisa gudunmawar da suka bayar wajen bunƙasa wannan babbar kafar yaɗa labarai.

Ya bayyana cewa tushen rediyo a Najeriya ya samo asali ne tun ranar 1 ga Afrilu, 1951 da aka kafa Nigerian Broadcasting Service domin ilmantarwa, fadakarwa da kuma haɗa kan al’umma. Daga bisani, a shekarar 1956 aka kafa Nigerian Broadcasting Corporation, kafin daga baya a shekarar 1978 aka haɗa tashoshin rediyo daban-daban aka samar da FRCN, wadda ake kira Radio Nigeria.

A cewarsa, FRCN ta samo asali ne daga ƙaramin tashar rediyo, amma yanzu ta zama babbar cibiyar watsa shirye-shirye mafi girma a nahiyar Afirka, wadda ke isar da sahihan labarai da shirye-shirye a sassa daban-daban na ƙasar.

Ya ƙara da cewa hukumar ta ci gaba da riƙe gaskiya da ƙwarewa a aikin jarida, tana ba da labarai da ke nuna halin da ƙasa ke ciki—daga ƙalubale zuwa nasarori—tare da ƙarfafa haɗin kai da zaman lafiya tsakanin al’umma.

Game da cigaban fasaha, Darakta Janar ɗin ya ce cigaban zamani ya taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa aikin rediyo, ciki har da ƙaddamar da tashoshin FM, amfani da fasahar dijital da kuma haɓaka manhajojin yanar gizo domin isar da saƙonni cikin sauƙi.

Sai dai ya jaddada cewa har yanzu akwai ƙalubale da suka haɗa da ƙarancin wutar lantarki, tsofaffin kayan aiki da kuma buƙatar ƙarin horar da ma’aikata domin su dace da sabbin fasahohi.

Dr Bulama ya tabbatar da cewa duk da waɗannan ƙalubale, FRCN za ta ci gaba da taka rawar gani a matsayin ginshiƙi na haɗin kan ƙasa, tare da shiga sabon zamani bayan cika shekaru 75 da kafuwa.

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai7 days ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara