Labarai
Gwamna Idris Ya Ba da Umarnin Binciken Gobarar da Ta Tashi a Makarantar Nurul Haqq da ke Birnin Kebbi
Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya bayar da umarnin gaggauta kafa wani kwamitin bincike mai ƙarfi domin gano musabbabin gobarar da ta tashi a Makarantar Nurul Haqq Quranic and Arabic School da ke Birnin Kebbi.
Lamarin, wanda ya faru a daren Asabar, ya shafi dakunan kwanan ɗalibai da kuma azuzuwa da dama a harabar makarantar. Gwamnan ya jagoranci sa ido kan ayyukan ceto da kashe gobarar a wurin da lamarin ya auku.
Yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa buda baki a watan Ramadan, gwamnan ya hango hayaƙi mai yawa a gefen hanya, inda nan take ya umarci ayarinsa da su tsaya domin gano inda hayaƙin yake fitowa. Daga bisani aka gano cewa daga harabar makarantar ne hayaƙin ke tashi.
Nan take ya bayar da umarnin kwashe dukkan ɗaliban makarantar tare da tuntubar Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kebbi da sauran jami’an agajin gaggawa domin shawo kan lamarin cikin hanzari. Kasancewarsa a wurin da kuma saurin ɗaukar matakinsa ya taimaka wajen fara aikin ceto ba tare da ɓata lokaci ba.
Nasir Idris ya ci gaba da kasancewa a wurin har zuwa ƙarshen aikin, inda ya rika sa ido kan yadda ake fitar da ɗalibai sama da 140 daga cikin haɗari, tare da tabbatar da cewa an kashe gobarar gaba ɗaya. Ya fifita tsaro da jin daɗin yaran fiye da duk wani jin daɗinsa na kai.
Gwamnan ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici, tare da gode wa Allah Maɗaukakin Sarki da cewa babu asarar rai. Ya kuma lura cewa kasancewar tankunan gas a wasu dakunan ɗalibai ya ƙara tsananta gobarar, wadda jami’an kashe gobara suka kwashe kusan awa uku zuwa huɗu suna fafatawa da ita.
Ya yabawa Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kebbi bisa gaggawar amsa kira, ƙwarewa da jajircewa wajen shawo kan lamarin. Haka kuma ya bai wa iyaye da masu kula da ɗalibai tabbacin cewa dukkan waɗanda abin ya shafa suna cikin koshin lafiya, kuma an mayar da su zuwa babban reshen makarantar.
Gwamnan ya jaddada cewa kwamitin binciken da aka kafa zai zurfafa bincike kan musabbabin faruwar lamarin tare da bayar da shawarwarin da suka dace domin hana aukuwar irin haka a makarantu a fadin jihar.
Sani Haruna?Kebbi
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai4 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
