Labarai
Wata Kungiya Ta Raba Kayan Abinci Ga Fursunoni A Wamba
Wata ƙungiyar agaji mai suna Islamic Society of Eggon-land (ISE) ta bai wa fursunoni da ke Cibiyar Gyaran Hali ta Wamba kayan abinci na sahur da buɗa-baki da darajarsu ta kai miliyoyin naira.
Yayin da yake miƙa kayan, Babban Sakataren ƙungiyar, Alhaji Umar Abdullahi Galle, ya bayyana cewa wannan tallafi wani ɓangare ne na al’adar da ƙungiyar ke yi a duk watan Ramadan domin tallafa wa ƙoƙarin gwamnati tare da kyautata jin daɗin fursunoni da inganta lafiyarsu yayin da suke zaman hukunci.
Ya ce manufar wannan tallafi ba wai rage ƙimar abin da gwamnati ke yi ba ne, sai dai don ƙara musu farin ciki da jin daɗi. Ya jaddada cewa kayan abincin ba na Musulmi kaɗai ba ne, an tanade su ne domin dukkanin fursunoni da ke zaman hukunci, kamar yadda kowa ke buƙatar buɗa-baki a wannan wata mai alfarma.
Alhaji Umar Abdullahi Galle ya kuma roƙi shugabannin cibiyar da su yi amfani da kayan yadda ya dace, domin ci gaba da kyakkyawar dangantaka da ake da ita. Ya tunatar da cewa sun ziyarci cibiyar a bara, inda suka samu kyakkyawan rahoto daga fursunoni kan yadda aka sarrafa tallafin da aka bayar a wancan lokaci, tare da kira ga shugabannin da su ci gaba da wannan kyakkyawan tsari.
Da yake karɓar kayan, Shugaban Cibiyar Gyaran Hali ta Wamba, John Ali-Bando, ya nuna godiya ga ƙungiyar Islamic Society of Eggon-land (ISE) bisa wannan karamci, tare da alƙawarin amfani da kayan yadda ya dace domin amfanin fursunonin.
Ya kuma yi kira ga sauran ƙungiyoyin agaji da na addini da su yi koyi da irin wannan aiki domin taimaka wa masu buƙata da inganta yanayin cibiyoyin gyaran hali a ƙasar.
COV/Aliyu Muraki/Lafia.
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai21 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai24 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
