Labarai
Gwamnatin Tarayya Ta Fara Aikin Sake Gina Gadar Namnai A Taraba
Gwamnatin Tarayya, ta hannun Hukumar Raya Yankin Arewa maso ta fara aikin sake gina gadar Namnai da ta rushe a Jihar Taraba.
Wannan babbar hanya mai yawan zirga-zirga, wadda ke haɗa jihar da yankunan kudancin Nijeriya, na cikin Ƙaramar Hukumar Gassol a jihar.
Abin tunawa ne cewa ambaliyar ruwa ta shekarar 2024 ce ta wanke gadar, lamarin da ya katse muhimmin hanyar sufuri tare da jefa masu amfani da hanya cikin wahala. Haka kuma, a sakamakon rushewar gadar a shekarun baya, an rasa rayuka da dama bayan aukuwar haɗurran jiragen ruwa (ƙananan kwale-kwale).
A halin da ake ciki, wata babbar tawaga daga NEDC, wadda ta ziyarci Jihar Taraba a ƙarshen mako domin ƙaddamar da ayyukan da ta aiwatar a faɗin jihar, ta kai ziyara wurin gadar domin duba yadda aikin ke tafiya.
Tawagar ta samu jagorancin Ministan Ƙananan Harkokin Raya Yankuna, wanda kuma ɗan asalin jihar ne, Hon. Uba Maigari Ahmadu. A cikin tawagar akwai Shugaban Kwamitin Gudanarwa na NEDC, Manjo Janar Paul Tarfa; Darakta Janar/ Shugaban Zartarwa na Hukumar, Mohammed Goni Alkali; ’yan Majalisar Dokoki ta Ƙasa; Daraktocin Zartarwa; mambobin Kwamitin Gudanarwa; da manyan jami’an gudanarwa na hukumar.
Da yake magana da ’yan jarida, Ministan ya ce ziyarar duba aikin na da nufin tantance ci gaba, ganin cewa tuni aka tura ’yan kwangila domin kammala aikin cikin gaggawa, don rage wa masu amfani da hanyar wahalhalu.
Hon. Uba Maigari Ahmadu ya bayyana cewa sake gina gadar da sauran ayyuka masu yawa da NEDC ta aiwatar a faɗin Jihar Taraba sun yi daidai da Manufar “Renewed Hope” ta Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
Ministan ya nuna farin ciki da fara aikin gadar a ƙarshe, tare da jaddada ƙudurin Shugaba Tinubu na samar da romon dimokuraɗiyya ga yankin da ƙasar nan baki ɗaya.
A nasa ɓangaren, Darakta Janar na NEDC, Mohammed Goni Alkali, ya bayyana tsoma-bakin a matsayin abin da ya zama dole domin rage wahalhalun da rushewar gadar ta haifar da kuma farfaɗo da harkokin tattalin arziki a yankin.
Ya sake tabbatar da jajircewar hukumar wajen hanzarta aiwatar da ayyukan raya kasa a yankin Arewa maso Gabas.
Wasu ’yan Nijeriya da ke yawan bin wannan hanya, a zantawarsu da wakilinmu, sun bayyana farin cikinsu da fara aikin ginin gadar, tare da yaba wa NEDC bisa cika aikinta.
Sani Sulaiman
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai4 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
