Labarai
Sojojin Nijeriya Sun Ceto Mutane 70 da Aka Yi Garkuwa da Su a Jihar Neja
Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Neja, Barista Abdulmalik Sarkin-Daji, ya yaba wa Rundunar Sojin Nijeriya bisa jagorantar wani gagarumin aikin tsaro da ya kai ga ceto kimanin mutane 70 da aka yi garkuwa da su a wasu sassan jihar.
Ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da Mukaddashin Shugaban Sashen Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a, Mairo Adamu Mani, ya sanya wa hannu kuma ya fitar ga manema labarai a Minna.
Abdulmalik Sarkin-Daji ya kuma yabawa Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) da sauran hukumomin tsaro bisa kyakkyawar haɗin kai da goyon bayan da suka bayar, wanda a cewarsa ya taimaka matuƙa wajen samun nasarar aikin tsaron da aka gudanar a Karamar Hukumar Mariga da sauran sassan Yankin Sanatan Arewa na Jihar Neja.
Ya bayyana aikin a matsayin babban sauƙi ga al’ummomin da abin ya shafa, inda ya jaddada cewa jarumtaka da ƙwarewar Rundunar Sojin Nijeriya tare da sauran hukumomin tsaro ne suka hallaka wasu ‘yan bindiga, kama wasu da ake zargi da aikata laifuka, da kuma ceto mutane da dama marasa laifi da aka tsare.
A cewarsa, ceto kimanin mutane 70 da aka yi garkuwa da su ya nuna ƙudurin da sojojin Nijeriya da sauran hukumomin tsaro suka ɗauka na kawo ƙarshen ‘yan bindiga da sauran ayyukan ta’addanci a jihar.
Abdulmalik Sarkin-Daji ya ƙara da cewa nasarar aikin ta farfaɗo da fata da kwarin gwiwa a zukatan mazauna jihar, musamman a yankunan karkara da masu rauni da suka sha fama da hare-hare da sace mutane. Ya kuma tabbatar wa Rundunar Sojin Nijeriya da sauran hukumomin tsaro da ci gaba da samun goyon baya da haɗin kai daga Gwamnatin Jihar Neja.
PR Aliyu Lawal
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai4 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
