Labarai
Rundunar Soja Ta Ƙaddamar da Aiki A Jihar Kwara
Dakarun Bataliya ta 22 ta Rundunar Sojin Najeriya, tare da gagarumin goyon bayan Ofishin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro na Ƙasa (ONSA), sun samu nasarar kwato Garin Dandi, wanda aka san shi a matsayin mafakar ’yan bindiga, a Ƙaramar Hukumar Ifelodun ta Jihar Kwara.
A cikin wata sanarwa da Kyaftin Maureen Ogbuka ta fitar a madadin Mukaddashin Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na Rundunar Sojin Sashe na 2, Rundunar Sojin Najeriya / Sashe na 3 na Ayyukan FANSAN YAMMA, ta bayyana cewa dakarun sun ci gaba da kai hare-hare masu tsari da haɗin kai kan ’yan ta’adda a cikin yankin ayyukan haɗin gwiwa, inda suka samu gagarumar nasara a wannan lokaci.
Sanarwar ta ce nasarorin da aka samu na nuna saurin ɗaukar mataki da jajircewar dakarun wajen tarwatsa hanyoyin sadarwa da ayyukan ’yan ta’adda.
Ta ƙara da cewa dakarun sun kashe wani ɗan ta’adda, yayin da wasu suka tsere zuwa cikin daji, ana zargin sun jikkata sakamakon harbin bindiga.
Haka kuma, sanarwar ta ce dakarun sun kai farmaki kan wasu sansanonin ’yan ta’adda da ke wurare masu nisa, waɗanda a baya jami’an tsaro ba su iya kaiwa ba. A yayin farmakin, an lalata sansanonin da aka bari da kuma kayayyakin tallafin aiki na ’yan ta’adda, lamarin da ya rage musu ƙarfin ci gaba da aikata ta’addanci.

Sanarwar ta yi kira ga al’umma da su ci gaba da bai wa hukumomin tsaro sahihan bayanai cikin lokaci game da ’yan bindiga da masu ba su haɗin kai, domin ƙarfafa ayyukan da ake ci gaba da gudanarwa a ciki da wajen Jihar Kwara
Ali Muhammad Rabiu
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai4 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
