Labarai
Kwamishiniyar Harkokin Mata Ta Kai Ziyarar Ta’aziyya ga Iyalan da Aka Kashe Mutane Bakwai
Kwamishiniyar Harkokin Mata, Yara da Masu Bukata ta Musamman ta Jihar Kano, Hajiya Amina Abdullahi Sani, ta kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan mutane bakwai da aka kashe kwanan nan a gidansu da ke unguwar Dorayi.
A yayin ziyarar, kwamishiniyar ta bayyana matuƙar kaduwa da alhini, inda ta bayyana kisan a matsayin babbar asara ga iyalan da abin ya shafa, al’ummar yankin, da ma Jihar Kano baki ɗaya.
Hajiya Amina ta nuna alhini na musamman kan mutuwar yara shida da mahaifiyarsu, tana mai cewa wannan mummunan lamari ya bar tabo mai zurfi a zukatan duk wanda ya ji labarinsa.
Ta ce, “Ya isa haka. Dole ne a dakatar da waɗannan munanan abubuwa da ke faruwa a jihar.”
Kwamishiniyar ta yi addu’ar samun rahamar Allah ga rayukan mamatan, tare da roƙon Allah Ya ba iyalan da suka rasa haƙuri da juriyar wannan babban rashi. Ta kuma yi kira ga al’umma, iyalai da hukumomin da abin ya shafa da su kasance masu faɗakarwa da ɗaukar matakan kariya wajen kare rayuka da dukiyoyi, tana mai jaddada cewa hana faruwar irin wannan masifa na buƙatar haɗin kai na kowa da kowa.
Hajiya Amina ta kuma tabbatar da ƙudirin ma’aikatarta na ci gaba da karewa da bunƙasa jin daɗin mata, yara da masu buƙata ta musamman. Ta bayyana cewa ana ci gaba da haɗin gwiwa da hukumomin tsaro da shugabannin al’umma domin ƙarfafa tsaro da walwalar zamantakewa.
Kwamishiniyar ta yaba wa Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, bisa jagoranci mai tausayi da kula da jama’a, musamman yadda yake jajircewa wajen tallafa wa masu rauni a cikin al’umma.
Domin tallafa wa iyalan da abin ya shafa, kwamishiniyar ta bayar da kayan abinci domin rage musu raɗaɗin wannan lokaci mai wuya. Ta samu rakiyar Mukaddashin Sakatare na Dindindin, Muhammad Sambo Iliyasu, da daraktocin ma’aikatar.
Rel/Khadijah Aliyu
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai24 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
