Ilimi
Ƴan Bindiga Sun Sace Dalibai da Malamai a Jihar Neja
Ƴan ta’adda sun kai hari Makarantar St. Mary’s da ke ƙauyen Papiri, a ƙaramar hukumar Agwara da ke Jihar Neja a Najeriya, inda suka yi garkuwa da ɗalibai da ma’aikatan makaranta da ba a tantance adadinsu ba zuwa yanzu.
Rahotanni daga makarantar sun ce harin ya faru ne da tsakar dare, kuma tuni aka fara tattara bayanai domin gano yawan mutanen da aka sace.
Wata majiya daga cocin Katolika a jihar ta tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai, inda ta ce har yanzu ana tattara bayanai kuma za a fitar da sanarwa nan gaba.
Kawo yanzu Jami’in hulɗa da jama’a na Rundunar ƴan Sandan Neja, SP Wasiu Abiodun, ya ce ana ci gaba da tattara bayanai, kuma daga bisani zasu fitar da cikakken bayani.
Shugaban sashen bada agajin gaggawa na ƙaramar hukumar Agwara, Ahmed Abdullahi Rofia, ya tabbatar da cewa ƴan ta’addan sun kutsa makarantar ne tsakanin ƙarfe 2:00 na dare zuwa 3:00 na dare, kuma a yanzu haka ana ci gaba da tantance adadin ɗalibai da ma’aikatan da aka yi garkuwa da su.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
