Kasuwanci
An Bukaci Manoman Kano Su Shiga Baje Kolin Kayan Noma Na Kasa
Hukumar Noma da Raya Karkara ta Jihar Kano (KNARDA) ta yi kira ga manoma da masu ruwa da tsaki a harkar noma da masu kirkire-kirkire a jihar da su shiga baje kolin noma na kasa da ke tafe.
A cikin wata sanarwa da Sashen Kula da Ayyukan Yada Labarai, KNARDA ya fitar, ta bayyana taron a matsayin wani babban dandali na baje kolin kayayyakin amfanin gona, da fasahohin zamani, da ke inganta samar da abinci da raya karkara.
Hukumar ta ja hankalin daidaikun jama’a da kungiyoyi a Kano da su yi amfani da wannan damar wajen gabatar da nasarorin da suka samu da kuma gano sabbin hanyoyin kasuwanci a fannin noma.
KNARDA ta kuma jaddada aniyar ta na tallafawa kokarin da ke inganta ayyukan noman zamani da ci gaban karkara.
Abdullahi Jalaluddeen/Kano
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai1 day ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
