Labarai
Kudurorin Kafa Hukumomi 3 Sun Tsallake Karatu Na 2 A Majalisar Dokokin Jihar Jigawa
Wasu kudurori guda 3 da ke dauke da bukatun kafa wasu hukumomi 3 sun samu karatu na biyu a zauren majalaisar dokokin jihar Jigawa.
Kudurorin guda 3 sun hada da na kafa Hukumar Samar da Hanyoyin Mota a yankunan karkara, da na kafa Hukumar Samar da Kudade Domin Ayyukan Hanyoyin Mota a yankunan karkara da Kuma na Hukumar Bunkasa Kwazon Malamai ta jihar Jigawa.
A lokacin ya ke gabatar da kudurorin domin neman goyon baya kan bukatar kafa hukumar bunkasa kwazon malamai, mataimakin shugaban masu rinjaye na majlaisar, Alhaji Sani Sale Zaburan ya ce gwamnatin jihar na da nufin inganta aikin koyarwa ta hanyar kafa hukumar da za ta rinka horas da malamai akai akai.
Da su ke tattaunawa kan wannan batu, wakilan mazabar Kanya Babba da na Fagam da na Sule Tankarar da na Guri, sun lura cewa kafa wannan hukumar zai maye gurbin ayyukan kwalejin horas da malamai da aka rushe a can baya, abin da zai kawo ingancin harkonin koyo da koyarwa a halin yanzu.
Kazalika da ya ke gabatar da kudurin neman goyon baya kan batun kafa hukuma da kuma asusun samar da hanyoyin mota a yankunan karkara, mataimakin shugaban masu rinjaye na majalisar, Alhaji Sani Sale Zaburan ya ce daukar wannan mataki zai karfafa yunkurin gwamnatin jihar na inganta harkokin sufuri ga jama’ar karkara.
Da su ke bada gudummawa kan wannan batu, wakilin mazabar Gwaram da na Kiri Kasamma da na Guri da kuma wakilin mazabar Fagam sun bayyana kudurorin biyu a matsayin wata alama da ke nuni da kyakkyawan kudurin gwamnatin Malam Umar Namadi wajen samar da hanyoyin mota ga yankunan karkara, inda fiye da kaso 60 na jama’ar jihar ke zaune.
Bayan samun goyon baya da gagarumin rinjaye sai aka yiwa kudurorin 3 karatu na 2, daga nan kuma shugaban majalisar dokokin jihar, Alhaji Haruna Aliyu Dangyatin ya mika kudurori 2 na hanyoyin mota a yankunan karkara ga kwamatin muhalli, yayin da kudurin kafa hukumar inganta kwazon malamai ya je ga kwamatin ilimi mai zurfi da na ilimi matakin farko, wanda dukkan su aka bai wa makonni 4 domin mika rahotannin su.
Usman Mohammed Zaria
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai20 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai23 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
