Ilimi
Zamfara Ta Yi Gargadi Akan Yiwa Shirinta Na Bunkasa Ilimi Zagon Kasa
Gwamnatin jihar Zamfara ta yi gargadin cewa ba za ta lamunci duk wani aiki na sakaci ko zagon kasa da zai iya kawo cikas ga kokarin da take yi na gyara da inganta harkar ilimi.
Shugaban hukumar kula da ilimin bai daya ta jihar Zamfara (ZSUBEB), Farfesa Nasir Garba Anka ne ya yi wannan gargadin a wata ziyarar bazata a makarantar firamare ta UBE, Low Cost da ke Gusau, biyo bayan rahotannin sace-sace da kuma lalata kadarorin gwamnati.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar, Ibrahim Maizare ya bayyana haka a wata sanarwa da ya ba rediyon Najeriya a Gusau.
Farfesa Nssiru Anka ya nuna matukar damuwa kan rashin kyawun kayan aiki, ya kuma bayyana lamarin a matsayin abin takaici.
A wata ziyarar bazata da ya kai makarantar, Farfesa Nasir Garba Anka ya gano cewa an kwashe wasu kayayyaki da suka hada da kujeru, tebura, da tagogi, ko kuma an lalata su.
Ya kuma bayyana faruwar lamarin a matsayin babban sakaci, ya kuma sha alwashin ganin an gurfanar da duk wadanda suka aikata laifin a gaban kuliya.
Nan take Farfesa Nasir Anka ya ba da umarnin a kama shugaban makarantar da jami’an tsaron makarantar domin yi masa tambayoyi don sanin yadda irin wannan barna ta faru a karkashin kulawarsu.
Farfesa Anka ya nanata kudirin hukumar na kare dukiyoyin jama’a da kuma samar da yanayi mai kyau na koyo a dukkan makarantun gaba da sakandare a fadin jihar Zamfara.
REL/AMINU DALHATU
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai1 day ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
