Ilimi
An Shawarci Iyaye Su Bari A Yiwa ‘Ya’yansu Alluran Rigakafi A Jigawa
An shawarci mata a karamar hukumar Kirikasamma da ke jihar jigawa da su kawo ‘ya’yansu domin yi musu rigakafin cutar shan inna, kyanda, da Gaida da sauran cututtuka masu ban tsoro.
Uwargidan Shugaban Karamar Hukumar, Hajiya Fatima Maji Marma ta ba da wannan shawarar a lokacin kaddamar da shirin rigakafin cutar kyanda da na rigakafi na yau da kullum a fadar Hakimin Marma.
Ta kuma jaddada aniyar karamar hukumar na bayar da tallafin da ake bukata domin samun nasarar gudanar da aikin rigakafin.
Hajiya Fatima ta kuma yabawa gwamnatin jihar Jigawa bisa bullo da inshorar lafiya ga marasa galihu a matakin unguwanni a kananan hukumomin jihar 27.
A nasa jawabin manajan hukumar kula da lafiya matakin farko na karamar hukumar Kabiru Musa Jahun ya bayyana jin dadinsa da yawan fitowar mata masu shayarwa da suke kawo jariransu domin yi musu rigakafin.
Shima da yake nasa jawabin Hakimin kauyen Marma, Alhaji Haruna Adamu, ya bayyana jin dadinsa kan sadaukarwar Hajiya Fatima Marma.
USMAN MZ
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai24 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
