Connect with us

Kasuwanci

Sardaunan Ikulu Ya Nemi Matasa da Mata su Shiga Siyasa Cikakke

Published

on

Daga Abdullahi Usman, Kaduna

Sardaunan Ikulu, Alhaji Dr. Isma’īl Yusuf Ashafa, ya kira mata da matasa a garin Ikulu da su shiga harkokin siyasa domin kawo ci gaba a yankinsu.

Ya fadi hakan ne a lokacin Taron Ikulu da aka shirya a Kaduna karkashin jagorancin Ikulu Political Forum (IPF). Ya jaddada cewa babu wata al’umma da za ta bunkasa sai an samu hadin kai tsakanin jama’a da kuma cikakkiyar rawar da matasa da mata ke takawa a siyasa.

Ya kara da cewa wajibi ne a wayar da kan matasa da mata, a ilimantar da su, sannan a motsa su su gane muhimmancin jagoranci ta hanyar jam’iyyun siyasa. Hakazalika, ya gargadi ‘yan siyasa a yankin da su guji “siyasar do ko mutu,” domin tabbatar da ci gaba da zaman lafiya a yankin.

Ya ce, soyayya, kishin ƙasa, da burin zaman lafiya ya kamata su kasance ginshiƙan jama’ar Ikulu.

A nasa jawabin, Shugaban Ƙungiyar Ci Gaban Ikulu (Ikulu Development Association – IDA), Mista Bature S. Likoro, ya jaddada muhimmancin zaman lafiya da ɗorewar haɗin kai a ƙasar Ikulu, tare da kiran shugabanni su mai da hankali kan ci gaban matasa da mata.

Sarauniyar Ikulu, Mrs. Lorentia Bature, ta bayyana cewa idan mata suka nesanta kansu daga siyasa, al’umma ba za ta ci gaba ba. Ta yabawa Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, saboda ayyukan ci gaba da yake aiwatarwa, tare da godewa Sardaunan Ikulu, Dr. Isma’īl Yusuf Ashafa, saboda jajircewarsa wajen tallafawa jama’arsa.

Comrade Moses Obadiah, Shugaban Kwamitin Shirya Taro, ya gargadi ‘yan siyasa da su guji siyasar addini, kabilanci da son kai, domin wadannan abubuwa suna haifar da rabuwar kai da koma-baya. Ya bayyana cewa Ikulu Youths Political Forum ta kafa haɗin kai da jam’iyyun siyasa domin inganta dimokuradiyya mai zaman lafiya.

Shugaban Ikulu Youths Political Forum, Mista Mathew Makama, ya bayyana cewa ƙasar Ikulu tana da mutanen kirki, masu gaskiya da kwazo, waɗanda ke son haɗin kai da gaskiya. Ya jaddada cewa zaman lafiya shi ne ginshiƙin ci gaban al’umma.

Mrs. Martina Sunday, shugabar mata, ta ƙarfafa mata da su yi sana’o’in halal domin dogaro da kai. Ta kuma yabawa Ikulu Youths Political Forum saboda ƙoƙarinsu na bunƙasa zaman lafiya da haɗin kai.

Honourable Justina Joseph Usman, Kansilan Ikulu Ward a karamar hukumar Zangon Kataf, ta gode wa Gwamna Uba Sani saboda ƙoƙarinsa na haɗa kan al’umma, tare da bayyana fatan cewa taron zai ƙara ɗaure zumunci da kawo ci gaba a yankin.

Mista Destiny Madaki, jami’i a Ikulu Political Forum, ya ce taron an shirya shi ne domin haɗa ‘ya’yan ƙasar Ikulu don ci gaban al’umma.

Mrs. Asabaru Yaro, memba a Kwamitin Amintattu na Ikulu Development Association, ta bukaci mata su ci gaba da kasancewa masu haɗin kai da tallafawa juna, sannan ta roƙi matasa su kasance masu zaman lafiya, haƙuri da fahimta domin ƙara ɗaukaka yankin.

Labarai

Labarai2 hours ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi1 week ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Mafi Shahara